Manyan shugabannin hukumomin tsaro a Kano sun taru a wata ƙaramar fada wacce Alhaji Aminu Ado Bayero ke zaune a cikinta a birnin Kano. Wannan lamari dai ya biyo bayan mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II da Gwamna Abba Yusuf ya yi kan kujerarsa, wanda ya koma fadar da ke Kofar Kudu a daren yau Asabar.
Sai dai Sarki Aminu Ado Bayero ya koma Kano a wani yanayi mai cike da ban mamaki sakamakon bayan tsige har da hana shi shiga jihar aka yi saboda gujewa hargitsin Sarki biyu a gari ɗaya.
- Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare
- Hukumomin Tsaro A Kano Sun Ƙi Biyayya Ga Umarnin Gwamnan Kano
Gwamna Yusuf ya bayar da umarnin a kamo Aminu Ado Bayero, inda ya zarge shi da yunƙurin ta da zaune tsaye. Duk da haka rundunar ‘yansandan jihar ta bayyana cewa za ta bi umurnin wata kotu da ta hana a dawo da Sarki Sanusi har sai an kammala sauraren ƙarar da aka kai gabanta.
A yau an ga duk wasu shugabannin jami’an tsaro yayin wata ganawa da Sarki Aminu Ado a ƙaramar fadar Kano da ke Nassarawa.
Yau dai abubuwan da yawa ka iya faruwa a Kano ciki har da batun sake mayar da Sarki Aminu Kano mulki da ƙarfin jami’an tsaro.