Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), ta gargadi ‘yan siyasa da su kauce wa yin kalamai marasa tushe yayin da ake kusantar zaben shugaban kasa.
Wannan na zuwa ne bayan da daraktan yakin neman zaben jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode, ya zargi sojoji da dan takarar shugaban kasa na PDP da yunkurin yin juyin mulki.
- ‘Yan Jihar Bauchi Sun Yabawa Buhari Kan Amincewa Da Ci Gaba Da Amfani Da Tsohuwar 200
- Baragurbin Ma’aikatan Banki Suka Jefa Talakawa Cikin Ƙunci – Buhari
DSS ta ce ya zama wajibi jam’iyyun siyasa da masu kula da kafofin yada labaransu su kaurace wa yada labaran karya a lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin isar da sakonsu ga magoya bayansu.
DSS ta ce irin wadannan bayanan marasa tushe na iya janyo martani mai zafi da kuma tada zaune tsaye.
Gargadin na zuwa ne biyo bayan binciken da hukumar ta yi wa daya daga cikin daraktocin yakin neman zaben jam’iyyar APC mai mulki Femi Fani-Kayode.
A shafin Twitter Fani-Kayode ya yi zargin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar da jami’an tsaro na shirin yin juyin mulki.
Hukumar ta yi wa Fani-Kayode tambayoyi ranar Laraba, sai dai nan take Muryar Amurka ba ta ji daga hukumar ta DSS ba na game da binciken.
Paul James, jami’in sa ido a harkar zabe na kungiyar YIAGA Africa mai zaman kanta, ya ce yin kalaman batanci a tsakanin jam’iyyun siyasa ba sabon abu bane.
“Hukumar DSS na binciken batun kuma ta kira Fani-Kayode don yi masa tambayoyi, mun zuba ido mu ga yadda zata kaya. Daga zaben jihar Ondo na shekarar 2020, mun ga abubuwa kamar haka. Sojoji suka fito karara suka musanta batun.
Amma akwai bukatar a fara yin abubuwan da zasu kawo kwarin gwiwa,” a cewar James a lokacin da ya zanta da wakilin Muryar Amurka Timothy Obiezu.
Yanzu a duk mako Fani-Kayode zai bayyana gaban hukumar DSS har sai an kammala bincike.
A ranar Litinin, ya yi magana da manema labarai a Abuja bayan da ya sha tambayoyi tsawon sa’o’i biyar, inda ya ce ya yi nadamar rubuta sakon a shafin Twitter ba tare da tabbatar da sahihancin batun ba daga hukumomi.
Najeriya na fuskantar karuwar yaduwar labaran karya gabanin babban zaben da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu, lokacin da kasar za ta kada kuri’a domin zaben sabon shugaban kasa, inda ‘yan takara uku ke kan gaba.