Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da manyan shugabannin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, a gaban Kotun Ƙoli ta Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba.
Mutanen su ne Mahmud Usman (wanda ake kira Abu Bara’a Abbas ko Mukhtar) da mataimakinsa, Mahmud Al-Nigeri (wanda aka fi sani da Malam Mamuda).
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata
- Amfani Da Karfin Tuwo Ba Zai Iya Kawo Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
Ana tuhumar su da zarge-zarge 32 da suka shafi ta’addanci a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite.
DSS ta ce waɗannan mutane ne suka kai harin gidan yarin Kuje a watan Yulin 2022, wanda ya bai wa fursunoni sama da 600 damar tserewa.
Haka kuma, ana tuhumar su da kitsa kai harin sansanin sojin Nijeriya na Wawa a Jihar Neja a 2022, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
DSS ta ce, shugabannin sun samu horo na musamman a kan amfani da makamai, dabarun yaƙi da kuma ƙera bama-bamai a ƙasashen Mali da Libya.
Ta ce Mamuda ya samu horo na musamman daga malamai masu tsattsauran ra’ayi a tsakanin 2013 da 2015.
Hakazalika, suna da hannu a sace manyan mutane, ciki har da sace wani Injiniya ɗan ƙasar Faransa, Francis Collomp a 2013 da kuma sace Alhaji Musa Umar Uba, Magajin Garin Daura a 2019.
Ana kuma zarginsu da fashi da makami da kuma shirin kai hari wajen wani haƙar uranium a Nijar, wanda shirin nasu bai yi nasara ba.
Mai Bai wa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu ne, ya tabbatar da kama su yayin wani samamen haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai.
Ribadu ya ce kama su zai kawo wa shugabancin ƙungiyar ta Ansaru koma baya.
Ansaru ta ɓalle daga cikin Boko Haram a 2012, inda da farko ta bayyana kanta a matsayin ƙungiya mai “tausaya wa al’umma.”
Amma daga baya ta haɗu da ƙungiyoyin ta’addanci na ƙasa da ƙasa, har ta ɗauki tambarin Al-Qaeda.













