Dubban magoya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar sun taru a wani filin wasa mai daukar mutum 30,000 a birnin Yamai a ranar Lahadi.
Magoya bayan sun hallara a filin wasan ne don nuna goyon bayansu ga gwamnatin soji a dai-dai lokacin da wa’adin mako daya da kungiyar ECOWAS ta gindaya wa sojojin Nijar na mayar da shugaban kasar Mohamed Bazoum kan karagar mulki.
Tawagar sojojin da suka yi juyin mulki, suma sun hallara filin wasan don nuna jin dadinsu da goyon bayan da ‘yan kasar suka basu.
A kwanakin baya da suka gabata, an ga matasan kasar dauke da tutocin Jamhuriyar Nijar da ta kasar Rasha suna nuna goyon bayansu ga juyin mulkin kasar inda suke adawa da gwamnatin Faransa.