Gwagwarmaya, jajircewa, rashin tsoro, duk wasu kalmomi ne da ake amfani dasu ne wajen yin bayani kan al’amarin daya shafi ganin sai an samu cimma wata manufa, gwagwarmayar ta siyasa sai an samu mai jajircewa ba tare da nuna tsoro ba domin kuwa idan aka fara yin ta akwai manyan matsalolin da mai da’awar kokarin yin hakan zai iya fuskanta cikin fafutukar ko gwagwarmayar da yake yi.
Ida ana maganar gwagwarmayar a duniya gaba daya ba za a taba mantawa da gudunmawar da marigayi Mista Mahatma Gandhi na Indiya,Zulfikhar Ali Bhutto, Benezir Bhutto Pakistan, Aung Suu Kyi ta kasar Myanmar, marigayi Dakta Kwame Nkurmah na Ghana, sai kuma nan gida Nijeriya ba zamu manta da wadanda suka yi gwagwamayar samun ‘yancin Nijeriya ba,domin sai kana da cikakken ‘yanci ne zaka samu damar yin harkokin siyasa ba tare da tsangwama ba.
- Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 3 A Wasu Birane
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Daina Muzgunawa Kamfanonin Waje
Mutane kamar su sir Abubakar Tafawa Balewa,Dakta Nmadi Azikiwe,Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato K.O Mbadwe,Chief Obafemi Owolwo,Malam Aminu Kano, da dai sauransu wadanda suka riga mu gidan gaskiya sai mu ce Allah ya jikansu ya rahamshe su.
Idan aka fara da Mahatma Gandhi jagoran siyasa na kasar Indiya ba a mantawa da irin gwagwarmayar da ya sha yi da Turawan mulkin mallaka wajen tabbatar da siyasar yadda ta kamata a kasar,ya sha wahalar gaske a hannun ‘yan mulkin mallaka nau’i daban- daban.Da haka ne har abin ya kai ga ‘yarsa Mrs Indira Gandhi ta gaje shi inda ta ci gaba daga wurin da mahaifinta ya tsaya, sannu a hankali har abin ya zo ya jikansa wato Mista Rajib Gandhi.
Idan kuma aka kalli kasar Pakistan kuma ana iya tunawa da su iyalan Bhutto kamar mulkin ya zama masu wata baiwa ce daga Allah.Dama su kasashen Indiya da Pakistan wadannda a shekaru masu yawa da suka gabata ana kiran kasar da sunan Indo- Pakisatan daga baya ne aka raba su a shekarar 1947, kowar ce daga cikinsu ta fara cin guminta. Zulfikar Ali Bhutto Lauya ne wanda ya taba Shugabantar kasar Pakistan ta mukamin Shugaban kasa da Firayim Ministan kasar har sau biyu daga 1971 zuwa 1973,sai kuma 1973 zuwa 1977 irin salon mulkin siyasa na kasashen Ingila da Amurka,sai ‘yarsa Benazir Bhutto ita ma ‘yar siiyasa ce matuka ta,Shugabanci kasar ta hanyar mukamin Firayim Minista ta 11,13, da 14,daga shekarun 1988 zuwa 1990,sai 1990 zuwa 1993, daganan sai 1993 zuwa 1996, daga karshe dai an yi mata kisan gilla ne. Aung San Suu Kyi ta kasar Myamar ‘yar gwagwamayar siyasa da kare hakkin dan Adam ta taba yin Shugabancin kasar Myamar,sanin kowa ne suna zaman manja da doya ne da hukumomin sojan kasar,an sha aikata gidan Fursunan kasar domin a halin da ake cikin yanzu tana gidan Kurkukun da zata share har shekara biyar,ba domin komai ba sai domin kare al’ummar kasar ta da take yi da kishinsu.
Marigayi tsohon Shugaban kasar Ghana Dakta Kwame Nkurmah daga shekarar1960 zuwa 1966,ya mutu ranar 27 Afrilu 1972 shine dan gwagwarmayar siyasa ne shi ma dan kishin kasa ne wanda yayi matukar suna ciki da wajen kasar Ghana
A kasar Nijeriya bayan da ‘yan kishin kasa suka yib ta fafutuka da gwagwarmayar samun ‘yancin kai,bayan an samu ‘yancin a shekarar 1960 dama an fara siyasa a karkashin kulawarTurawan mulkin mallaka na Ingila, akwai jam’iyyu da suka hada da NPC, NEPU, NCNC,da AG ko kuma jam’iyyar mutanen Arewa (Northern People Congress NPC) jam’iyyar matasan Arewa (Northern Element Progressibe Union NEPU) (National Council for Nigeria And Cameroun NCNC) ta al’umma kudu maso gabashin Nijeriya ce wato Ibo yayinda ita kuma (Action Group AG)ta al’ummar sashen Kudu maso yammcin Nijeriya ko Yarabawa.
Haka aka fara dama Furar a lokacin aka kuma ci gaba da shan ta hakanan sai dai kuma wani al’amari daban ‘yan jam’iyyar NEPU a lokacin wadda daga baya ta koma PRP kamar su marigayi Alhaji Wada Nas,Alhaji Musa Musawa, Alhaji Sa’adu Zungur,Khalifa Hassan Yusuf,da dai sauran manyan ‘ya’yan jam’iyyar sun sha gwgwarmayar siyasa wajen nemar maTalakawa ‘yancin kansu.
Alhaji Wada Nas Funtuwa a wata hirar da kafar yada labarai ta taba yi da shi ya ce yana taba tafiya kan Keke daga Funtuwa zuwa Kano saboda duk a cikin gwagwarmayar,madugun jam’iyyar ceton al’umma marigayi Malam Aminu Kano ya sha bakar azaba saboda akidarsa ta ganin suma Talakawa an basu dama suna bara gyada domin ai suna da Kunba.
Duk ta sanadiyar gwgwarmayar siyasa da aka yi babban zabe na shekarar1979 lokacin Nijeriya na da Jihohin goma sha tara jam’iyyar PRP a lokacin ta samu nasarar lashe zaben gwamnoni biyu daga cikin 19 ta samu Jihohin Kano da Kaduna ko shakka babu Jihohin biyu na da muhimmanci a siyasar Nijeriya,da farko dai Kaduna ita ce fadar Arewa daga cikin tane aka kirkiro Jihohi 18 na Arewa dalilin da yasa take da 19 ke nan a yanzu.
Allah ya jikansu da rahama yasa sun huta Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa da Alhaji Abubakar Rimi sun bada gaggarumar gudunmawa wajen ci gaban Jihohin musamman ma Muhammed Abubakar Rimi da aka fi sani da Limanin canji ya ci gaba daga inada marigayi Abdu Bako ya tsaya wanda ya fara dora tubalin bunkasar Jihar Kano.Shi marigayi Alhaji Abdulkadir Ballarabe Musa zamanin da yayi mulkin Jihar Kaduna bai samu damar mulki kamar yadda yake so ba a dalilin takin – sakar da ya rika yi da ‘yan majalisar Jihar Kaduna wadanda yawancinsu ‘yan jam’iyyar NPC a karkashin jagoranci Mamman Abubakar Danmusa wanda a lokacin shine Kakain majalisar Jihar.Daga karshe dai sai da suka tsige shi daga mukamin gwmanan Jihar.
Wani abinda ba za a taba mantawa da shi ba Jihohin biyu shine yadda gwamnonin biyu suka bada dokar hana biyan Haraji da Jangali,wanda sanin kowa ne sanadiyar biyan Haraji da Jangali Talakawan Arewa da yawa daga cikinsu sun bar garuruwansu domin lokacin Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya suna da matukar karfin mulkin sun gallazawa Talakawa matuka suka hana su sakat sanadiyar biyan Haraji da Jangali yayin da shi Haraji duk Talakawa na biya shi kuwa Jangali mafi yawa Fulani suke biya na Dabbobinsu,janye maganar biyan nau’oin Harajin ba karamin taimakawa Talakawa yayi ba.
Da haka ne abu na ta tafiya wato gwagwarmayar siyasa domin wasu su masu sa’ida har abin ya zo ga madugu uban tafiya Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya nuna a salon tafiyar da mulkinsa,yayi koyi da gwarazan manya wadanda suka kwanta dama sun yi gwagwarmayar siyasa da a lokacin tafi wadda yake yi yanzu wuya.Lokacin da ya zama gwamnan Jihar Kano da Sanata ya taimakawa Talakawa da da’yansu musamman ma ta bangaren ilmiin da ya tura wasu zuwa kasashen wajen suka yi karatu sun dawo gida Nijeriya sun zama wasu suna bada tasu gudunmawar.
Har ya zuwa lokacin daya fara neman takarar Shugaban kasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka yi Kwankwanso ya zo na uku,amma daga karshe ya sake komawa jam’iyyar PDP wanda har zuwa lokacin da aka yi babban zabe na 2019 yana da dan takarar gwamna na Jihar Kano Injiya Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Gida- gida.A zaben an yi gwagwagwa da gwagwarmaya tunda bayan zabe an fara bayyana sakamako na kananan hukumomi inda jam’iyyar PDP k e gaba, sai daga baya al’amarin ya zama da ba a kammala ba da ake ce ma inconclusibe.
Hausawa sun ce asha ruwa a koma aiki haka Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ci gaba da yi domin kuwa bayan ya sake fita daga jam’iyyar PDP ya kafa jam’iyyar siyasa har wasu nayi ma shi kallon ba zai iya zuwa ko ina ba,amma cikin ikon Allah Abba Gida—gida ya sake tsayawa takarar gwamna a karkashin jam’iyyar shi kuma ya tsaya takarar Shugaban kasa.
Bayan zaben Shugaban kasa dana ‘yan majalisun kasa jam’iyyar tana da Sanatoci 2 da ‘yan majalisar kasa 18, shi kuma ya samu nasarar lashe kuri’un Jihar Kano da gaggarumin rinjaye na fiye da 900,000,a zaben gwamnan da aka yi Asabar 18 Maris 2023 bayan da aka bayyana sakamako Injiniya Abba Kabir ya lashe zaben Jihar da kuri’u fiye da milyan daya abin ya zama conclusibe da aka kammala.Mahakurci watarana mawadaci ne kamar yadda masu iya magana suka cewa.