ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dubi Ga Amfanin Jajircewa A Gwagwarmayar Siyasa

by Idris Aliyu Daudawa
3 years ago
Siyasa

Gwagwarmaya, jajircewa, rashin tsoro, duk wasu kalmomi ne da ake amfani dasu ne wajen yin bayani kan al’amarin daya shafi ganin sai an samu cimma wata manufa, gwagwarmayar ta siyasa sai an samu mai jajircewa ba tare da nuna tsoro ba domin kuwa idan aka fara yin ta akwai manyan matsalolin da mai da’awar kokarin yin hakan zai iya fuskanta cikin fafutukar ko gwagwarmayar da yake yi.

Ida ana maganar gwagwarmayar a duniya gaba daya ba za a taba mantawa da gudunmawar da marigayi Mista Mahatma Gandhi na Indiya,Zulfikhar Ali Bhutto, Benezir Bhutto Pakistan, Aung Suu Kyi ta kasar Myanmar, marigayi Dakta Kwame Nkurmah na Ghana, sai kuma nan gida Nijeriya ba zamu manta da wadanda suka yi gwagwamayar samun ‘yancin Nijeriya ba,domin sai kana da cikakken ‘yanci ne zaka samu damar yin harkokin siyasa ba tare da tsangwama ba.

  • Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 3 A Wasu Birane
  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Daina Muzgunawa Kamfanonin Waje

Mutane kamar su sir Abubakar Tafawa Balewa,Dakta Nmadi Azikiwe,Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato K.O Mbadwe,Chief Obafemi Owolwo,Malam Aminu Kano, da  dai sauransu wadanda suka riga mu gidan gaskiya sai mu ce Allah ya jikansu ya rahamshe su.

ADVERTISEMENT

Idan aka fara da Mahatma Gandhi jagoran siyasa na kasar Indiya ba a mantawa da irin gwagwarmayar da ya sha yi da Turawan mulkin mallaka wajen tabbatar da siyasar yadda ta kamata a kasar,ya sha wahalar gaske a hannun ‘yan mulkin mallaka nau’i daban- daban.Da haka ne har  abin ya  kai ga ‘yarsa Mrs Indira Gandhi  ta gaje shi inda ta  ci gaba daga wurin da mahaifinta ya tsaya, sannu a hankali har abin ya zo ya jikansa wato Mista Rajib Gandhi.

Idan kuma aka kalli kasar Pakistan kuma ana iya tunawa da su iyalan Bhutto kamar mulkin ya zama  masu wata baiwa ce daga Allah.Dama su kasashen Indiya da Pakistan wadannda a shekaru masu yawa da suka gabata ana kiran kasar da sunan Indo- Pakisatan daga baya ne aka raba su a shekarar 1947, kowar ce daga cikinsu ta fara cin guminta. Zulfikar Ali Bhutto Lauya ne wanda ya taba Shugabantar kasar Pakistan ta mukamin  Shugaban kasa da Firayim Ministan kasar har sau biyu daga 1971 zuwa 1973,sai kuma 1973 zuwa 1977 irin salon mulkin siyasa na kasashen Ingila  da Amurka,sai ‘yarsa Benazir Bhutto  ita ma ‘yar siiyasa ce matuka ta,Shugabanci kasar ta hanyar mukamin Firayim Minista ta 11,13, da 14,daga shekarun 1988 zuwa 1990,sai 1990 zuwa 1993, daganan sai 1993 zuwa 1996, daga karshe dai an yi mata kisan gilla ne. Aung San Suu Kyi ta kasar Myamar ‘yar gwagwamayar siyasa da kare hakkin dan Adam ta taba yin Shugabancin kasar Myamar,sanin kowa ne suna zaman manja da doya ne da hukumomin sojan kasar,an sha aikata gidan Fursunan kasar domin a halin da ake cikin yanzu tana gidan Kurkukun da zata share har shekara biyar,ba domin komai ba sai domin kare al’ummar kasar ta da take yi da kishinsu.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

Marigayi tsohon Shugaban kasar Ghana Dakta Kwame Nkurmah daga shekarar1960 zuwa 1966,ya mutu ranar 27 Afrilu 1972 shine dan gwagwarmayar siyasa ne shi ma dan kishin kasa ne wanda yayi matukar suna ciki da wajen kasar Ghana

A kasar Nijeriya bayan da ‘yan kishin kasa suka yib ta fafutuka da gwagwarmayar samun ‘yancin kai,bayan an samu ‘yancin a shekarar 1960 dama an fara siyasa a karkashin kulawarTurawan mulkin mallaka na Ingila, akwai jam’iyyu da suka hada da NPC, NEPU, NCNC,da AG ko kuma jam’iyyar mutanen Arewa (Northern People Congress NPC) jam’iyyar matasan Arewa (Northern Element Progressibe Union NEPU) (National Council for Nigeria And Cameroun NCNC) ta al’umma kudu maso gabashin Nijeriya ce wato Ibo yayinda ita kuma (Action Group AG)ta al’ummar sashen Kudu maso yammcin Nijeriya ko Yarabawa.

Haka aka  fara dama Furar a lokacin aka kuma ci gaba da shan ta hakanan sai dai kuma wani al’amari daban ‘yan jam’iyyar NEPU a lokacin wadda daga baya ta koma PRP kamar su marigayi Alhaji Wada Nas,Alhaji Musa Musawa, Alhaji Sa’adu Zungur,Khalifa Hassan Yusuf,da dai sauran manyan ‘ya’yan jam’iyyar sun sha gwgwarmayar  siyasa wajen nemar maTalakawa ‘yancin kansu.

Alhaji Wada Nas Funtuwa a wata hirar da kafar yada labarai ta taba yi da shi ya ce yana taba tafiya kan Keke daga Funtuwa zuwa Kano saboda duk a cikin gwagwarmayar,madugun jam’iyyar ceton al’umma marigayi Malam Aminu Kano ya sha bakar azaba saboda akidarsa ta ganin suma Talakawa an basu dama suna bara gyada domin ai suna da Kunba.

Duk ta sanadiyar gwgwarmayar siyasa da aka yi babban zabe na shekarar1979 lokacin Nijeriya na da Jihohin goma sha tara jam’iyyar PRP a lokacin ta samu nasarar lashe zaben gwamnoni biyu daga cikin 19 ta samu Jihohin Kano da Kaduna ko shakka babu Jihohin biyu na da muhimmanci a siyasar Nijeriya,da farko dai Kaduna ita ce fadar Arewa daga cikin tane aka kirkiro Jihohi 18 na Arewa dalilin da yasa take da 19 ke nan a yanzu.

Allah ya jikansu da rahama yasa sun huta Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa da Alhaji Abubakar Rimi sun bada gaggarumar gudunmawa wajen ci gaban Jihohin musamman ma Muhammed Abubakar Rimi da aka fi sani da Limanin canji ya ci gaba daga inada marigayi  Abdu Bako ya tsaya wanda ya fara  dora tubalin bunkasar Jihar Kano.Shi marigayi  Alhaji Abdulkadir Ballarabe Musa zamanin da yayi mulkin Jihar Kaduna bai samu damar mulki kamar yadda yake so ba a dalilin takin – sakar da ya rika yi da ‘yan majalisar Jihar Kaduna wadanda yawancinsu ‘yan jam’iyyar NPC a karkashin jagoranci Mamman Abubakar Danmusa wanda a lokacin shine Kakain majalisar Jihar.Daga karshe dai  sai da suka tsige shi daga mukamin gwmanan Jihar.

Wani abinda ba za a taba mantawa da shi ba Jihohin biyu shine yadda gwamnonin biyu suka bada dokar hana biyan Haraji da Jangali,wanda sanin kowa ne sanadiyar biyan Haraji da Jangali Talakawan Arewa da yawa daga cikinsu sun bar garuruwansu domin lokacin Sarakunan gargajiya na Arewacin Nijeriya suna da matukar karfin mulkin sun gallazawa Talakawa matuka suka hana su sakat sanadiyar biyan Haraji da Jangali yayin da shi Haraji duk Talakawa na biya shi kuwa Jangali mafi yawa Fulani suke biya na Dabbobinsu,janye maganar biyan nau’oin Harajin ba karamin taimakawa Talakawa yayi ba.

Da haka ne abu na ta tafiya wato gwagwarmayar siyasa domin wasu su masu sa’ida har abin ya zo ga madugu uban tafiya Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya nuna a salon tafiyar da mulkinsa,yayi koyi da gwarazan manya wadanda suka kwanta dama sun yi gwagwarmayar siyasa da a lokacin tafi wadda yake yi yanzu wuya.Lokacin da ya zama gwamnan Jihar Kano da Sanata ya taimakawa Talakawa da da’yansu musamman ma ta bangaren ilmiin da ya tura wasu zuwa kasashen wajen suka yi karatu sun dawo gida Nijeriya sun zama wasu suna bada tasu gudunmawar.

Har ya zuwa lokacin daya  fara neman takarar Shugaban kasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka yi Kwankwanso ya zo na uku,amma daga karshe ya sake komawa jam’iyyar PDP wanda har zuwa lokacin da aka yi babban zabe na 2019 yana da dan takarar gwamna na Jihar Kano Injiya Abba Kabir Yusuf da aka fi sani  da Gida- gida.A zaben an yi gwagwagwa da gwagwarmaya tunda bayan zabe an fara bayyana sakamako na kananan hukumomi inda jam’iyyar PDP k e gaba, sai daga baya al’amarin ya zama da ba a kammala ba da ake ce ma inconclusibe.

Hausawa sun ce asha ruwa a koma aiki haka Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ci gaba da yi domin kuwa bayan ya sake fita daga jam’iyyar PDP ya kafa jam’iyyar siyasa har wasu nayi ma shi kallon ba zai iya zuwa ko ina ba,amma cikin ikon Allah Abba Gida—gida ya sake tsayawa takarar gwamna a karkashin jam’iyyar shi kuma ya tsaya takarar Shugaban kasa.

Bayan zaben Shugaban kasa dana ‘yan majalisun kasa jam’iyyar tana da Sanatoci 2 da ‘yan majalisar kasa 18, shi kuma ya samu nasarar lashe kuri’un Jihar Kano da gaggarumin rinjaye na fiye da 900,000,a zaben gwamnan da aka yi Asabar 18 Maris 2023 bayan da aka bayyana sakamako Injiniya Abba Kabir ya lashe zaben Jihar da kuri’u fiye da milyan daya abin ya zama conclusibe da aka kammala.Mahakurci watarana mawadaci ne kamar yadda masu iya magana suka cewa.

Siyasa
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Sarakunan Da Suka Yi Wa Turawan Mulkin Mallaka Turjiya A Nijeriya
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

MASU ALAKA

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC
Manyan Labarai

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa
Siyasa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci
Siyasa

Zaɓen 2027: NNPP Ta Fara Shigar Da Sunayen ’Yan Takara, Ta Nemi INEC Ta Ƙara Mata Lokaci

July 8, 2026
Next Post
A Karon Farko Iyayena Ba Su Amince Da Shigata Fim Ba —Fatima Moh’d

A Karon Farko Iyayena Ba Su Amince Da Shigata Fim Ba —Fatima Moh’d

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.