Oluremi Tinubu ta kasance uwargida ga sabon shugaban kasa wanda aka zakolushi a Jihar Legas da mijinta, Bola Tinubu a matsayin gwammna daga shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2007.
Ita ce ta wakilci yankin legas ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya daga shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2023.
Ta kasance mamba a jam’iyyar All progressibe Congress (APC), jam’iyyar siyasa na tsawon shekara fiye da 5.
Oluremi dai an haifeta ne a shekarar 1960, a ranar 21 ga watan Satumba, shekarunta kenan yanzu ya kai 62.
Oluremi Tinubu ta kasance ita Fasto kuma Sanatan wa’adi na uku wanda ta zama uwargidan shugaban Nijeriya.
Matsayin uwargidan shugaban kasa a Nijeriya shi ne wanda ake mutunta shi saboda muhimmiyar rawar da duk matar shugaban kasa take yi wa al’umma.
Oluremi Tinubu, matar da ke rike da mukami a halin yanzu mace daya ce mai karfi kuma ita kanta ‘yar siyasa ce.
Sunan Oluremi Tinubu ya riga ya shahara a cikin gwamnatin.
Ita ce Sanatan Nijeriya mai wakiltar mazabar Legas ta tsakiya a majalisar wakilai ta kasa sau uku. Tanada ‘ya’ya hudu: Folashade Tinubu-Ojo, Seyi Tinubu, Hide Tinubu,
Abibat Tinubu.
Ita dai Oluremi Tinubu tana rike da digirin digirgir a fannin ilimi, ta yi aiki a matsayin Malamar Sakandiri na wani dan karamin lokaci har sai da aka zabi mijinta Bola Tinubu a matsayin gwannan Jihar Legas bisa tafarkin dimokuradiyya a shekarar 1999. A matsayin matar gwamnan Jihar Legas, Oluremi Tinubu ta Shiga cikin lamarin. A cikin ayyukan zamantakewa a cikin Jihar Legas.
Sanata Oluremi malama ce, ta kasance malamar sakandare kafin ta shiga siyasa. Ta fara dandana siyasar Nijeriya lokacin da ta zama matar gwamnan Jihar Legas, mutane kuma suna sonta.
Oluremi Tinubu ‘yar Jihar Delta ce.
Oluremi Tinubu ‘yar siyasan Nijeriya ce kuma Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dokoki ta kasa.
Sunanta na gaskiya : Oluremi Shade Tinubu.
Sanata Oluremi Tinubu ta wakilci gundumar Legas ta tsakiya a karkashi jam’iyyar All progressibe Congress (APC).
Mutanan Legas sun bayyana salon Remi a matsayin mai nuna aji da bayyana kyawunta, yayin da kuma ta ke da saukin kai wajen yin mu’amalar ta.
Sanata remi Tinubu, an santa da salon kwalliya don nuna irin kyawun da ta ke da shi. Mace ce ‘yar siyasa mai kishi, wacce kyawawan halayenta a matsayinta na hazika mai kula da jama’a da taimakon jama’a.
Har ila yau, wata fitacciyar ‘yar jarida, Busola Kukoyi, ta ce wani abu da mutane ba su sani ba game da Misis Remi Tinubu shi ne tana da tausayi sosai.
A cewar, ku yi koyi da Remi ta tsani ganin yadda mutane ke shan wahala ko shiga kunci.