Duba da yadda ake a cikin matsin tattalin arziki da ake ci gaba da fuskanta a Nijeriya, an ruwaito cewa, bankuna sha biyu a kasar, sun samu gwagwabar ribar da ta kai ta Naira tiriyan 3.81 a zangon farko na 2024, bayan sun biya harajinsu.
Wannan ya nuna cewa, duk a lokaci irin wannan a 2023, bankunan sun samu karin da ya kai na kashi 108.2 daga cikin Naira tiriliyan 1.83.
- Li Qiang Ya Halarci Taron Majalisar Shugabannin Gwamnatocin Kasashe Mambobin SCO Karo Na 23
- Peng Liyuan Ta Taya Murnar Gudanar Da Bikin Bayar Da Lambobin Yabo Kan Bunkasa Ilimin Mata Da ‘Yan Mata Na UNESCO
Wadannan bankunan sha biyu da kamfanin hada-hadar musayar kudi ya zayyano, bayan sun biya harajinsu, sun samu ribar da ta kai ta Naira tiriliyan 3.808 a ranar 30 na watan Junin 2024.
Wadannan bankunan sune; GTCO, Zenith Fidelity, UBA, Access Holdings, Stanbic IBTC Holdings, FCMB Group, Wema Bank, FBNH.
Sauran sun hada da; bankin Jaiz Bank, Ecobank sai kuma Sterling Financial Holdings, wadanda bayan sun biya harajinsu, suka samu karin ribar Naira tiriliyan 1.979, ko kuma kashi 108.201, idan aka kwatanta da ribar da suka samu ta Naira tirilyan N1.829 a cikin rabin shekarar 2023.
Masu fashin baki a fannin hada-hadar bankuna sun sanar da cewa, wadannan bakunan sun samu wannan nasarar ce, saboda samun karin kudin ruwansu da kadarorinsu, wanda hakan ya sanya kudin ruwansu ya karu da kuma yadda takardar Naira ta na tashi tana sauka.
Bugu da kari, idan aka yi dubi a kan ribar da bankin GTCO ya wallafa ya samu a 2024, hakan ya nuna cewa, a bisa tarihi, bayan ya biya harajinsa, ribarsa ta karu zuwa kashi 206.6 wadda ta kai ta Naira tirliyan 1.004, sabanin ribar Naira biliyan 327.40, da ya samu a rabin shekarar 2023.
Shi kuwa bankin Zenith, bayan ya biya harajinsa, ya ayyana ya samu ribar Naira biliyan 727.030, wadda akalla ta karu zuwa kashi 107.51.
Bugu da kari, bankin UBA, bayan ya biya harajinsa, ya samu ribar da kai ta Naira 401.577 biliyan a cikin rabin shekarar 2024.
Shi ma bankin Fidelity, bayan ya biya harajinsa ya samu ribar da ta kai ta Naira biliyan 200.872.
Bakin Access Holdings, ya samu ribar Naira biliyan 348.922, Access Holdings Naira biliyan 202.7.
Hakazalila, Stanbic IBTC Holdings, ya samu ribar Naira bilyan 147, bankin FCMB, ya samu ribar Naira biliyan 64.209.
Bankin Wema, ya samu ribar Naira biliyan 30.565, sai kuma bankin FBNH da ya samu ribar Naira biliyan 411.990, bankin Jaiz, ya samu ribar Naira biliyan 11.562.
Har ila yau bankin ETI, ya samu ribar Naira biliyan 443.513, inda bankin Sterling Financial Holdings, ya samu ribar Naira 17.346.