Rahotanni na bayyana cewa, ‘yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare tare da kashe mutane da kuma sace dabbobi da dukiyoyin al’umma a wasu sassa na yankin Karamar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara.
A kusa-kusan nan, ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum biyar tare da raunata wasu mutum hudu a garin Galadi da ke karamar hukumar.
- NDLEA Ta Kama Kwalaben Akuskura Sama Da 8,000 A Kano
- ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Damfara A Kano
Wadannan hare-hare, na ci gaba da afkuwa duk kuwa da yunkurin yin sulhu da al’ummomin wasu garuruwa na Karamar Hukumar Shinkafin da ake yi da ‘yan bindigan da kuma matakan tsaro iri daban-daban da ake ci gaba da dauka.
Har ila yau, wannan atsala ta hare-haren ‘yan bindiga da ta zame wa yankin Arewa Maso Yamma tamkar wani karfen-kafa, na ci gaba da addabar garin Galadi da sauran kauyuka da dama da ke makwabtaka da shi a yankin Karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara. Kamar dai yadda wani mutumin yankin ya laburta.
“Wadannan ‘yan bindiga, sun kawo hari wani gari da ke kusa da mu mai suna Bargaja a ranar Litinin da ta gabata da rana tsaka, inda suka dauki mutane suna tsaka da aiki a cikin gonakinsu.
“Haka nan, ‘yan bindigan, suna sake kawo wani harin a wannan gari namu na Galadi da misalign karfe 10:15 na daren ranar Laraba, inda suka kewaye baki-dayan Galadin; illa bangare guda shi ma saboda gulbi ya tare wannan gefen ne, inda suka bude wa Galadin wuta ta kowane gefe baki-daya,” in ji shi.
Kazalika ya kara da cewa, “Babu shakka, wannan hari ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane biyar, inda kuma wasu hudu ke kwance a gadon asibiti. Sai dai, Allah cikin ikonsa ya sa ba su samu damar tafiya da ko mutum guda ba,sakamakon dauki da aka samu daga wasu jami’an tsaro da suka garzayo daga Shinkafi.
“Duk da cewa, a nan muna da jami’an tsaro; amma a lokacin da suka kawo wannan hari, sai da suka mamaye sansanin jami’an tsaron baki-daya,” kamar yadda ya bayyana.
Har wa yau, wannan Bawan Allah da ke wannan yanki na Galadi da ya nemi a sakaya sunansa ya kara da cewa; wadannan hare-hare na ci gaba da afkuwa, duk kuwa da shirin da al’ummomin yankin ke yi da kuma na gwamnatin tarayya, na tattaunawar sulhu da ‘yan bindigan.
Yayin da aka tuntubi babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan kafafen yada labarai, Mustafa Jafaru Kaura cewa ya yi; har yanzu matsayin gwamnatin jihar bai sauya ba game da kaucewa tattaunawa ko yin sulhu da ‘yan bindiga.
“Saboda haka, koda wani abu ya faru a wannan gari na Galadi, ko shakka babu, Gwamnatin Jihar Zamfara na matukar bakin ciki da faruwar al’amari, sannan kuma tana yin iya kokarinta wajen ganin an ci gaba da fatattakar wadannan barayi, don ganin Allah ya kawo mana saukin al’amarin.”
Bugu da kari, masana harkokin tsaro na ci gaba da yin tsokacin cewa; kokarin magance matsalar ta tsaro a yankin Arewa Maso Yammacin Nijeriya , abu ne da ke bukatar matakai irin na bai- daya.
Sannan kuma, wajibi ne a wadanda za a dauka a dauke su a lokaci guda, idan dai har ana so a ga karshen wannan matsala da ta ki ci ta ki cinyewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp