Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, Dakta Yusuf Yaqubu Alrigasiyu, ya bayyana cewa hukumar tana bukatar karin kujeru 500 na aikin hajjin bana (2023).
A wata zantawa da manema labarai a ranar Talata, Dakta Alrigasiyu ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ware wa jihar kujeru 5,987, inda ake sa ran maniyyatan za su biya Naira miliyan 2.919 a kowace kujera.
A cewarsa, bukatar karin ta zama dole ne don biyan bukatun sauran maniyyatan da ake sa ran za su biya kudin kujerun a jihar nan da kwanaki masu zuwa.
Ya kuma yi nuni da cewa, duk maniyyacin da ya biya kudin tafiyarsa, yana da hakkin samun alawus din kudin tafiya Dala 800.
Dakta Alrigasiyu ya kawo dalilai da dama da suka haddasa tashin farashin kudin kujerar wadanda suka hada da tsadar masaukai, karin farashin dala kan Naira, karin haraji zuwa kashi 15 cikin 100 da mahukuntan Saudiyya suka yi, da tsadar kudin man jiragen sama.
Ya ce duk da tashin farashin man, kudin kujerar aikin hajji a Nijeriya ya kasance mafi sauki a duniya.
Ya lissafo kasashe kamar Malaysia, Pakistan, Ghana, da Jamhuriyar Nijar, wadanda suka fi Nijeriya tsadar kudin kujerun aikin hajji.
Sakataren zartarwar ya nuna godiya ga shugabannin NAHCON na ganin cewa kudin kujerar ya gaza kasa da Naira Miliyan 3.