Gwamnatin Tarayya ta gargadi kamfanoni masu zaman kansu da cewar ka da su biya ma’aikatansu kasa da Naira 70,000 a matsayin albashi.
Gwamnatin ta ce duk kamfanin da aka samu na biyan ma’aikatansa kasa da haka, na iya jefa mahukuntan kamfanin a gidan yari.
- An Fitar Da Takardar Matsayar Sin A Taron Kolin MDD Kan Makoma Da Muhawarar Babban Taron MDD Karo Na 79
- Gandiroba Ya Hallaka Abokin Aikinsa Kan Abinci A Bauchi
A wani taron shekara-shekara da aka gudanar a Jihar Legas, Ma’aikatar Ayyuka da Ƙwadago ce ta yi gargadin.
Ma’aikatar Ayyuka da Kwadago ta jaddada cewa mafi karancin albashi a yanzu ya zama doka, kuma babu wani ma’aikaci a Nijeriya da za a biya kasa da hakan a matsayin albashi.
An bukaci kamfanonin masu zaman kansu da su tabbatar cewa ma’aikatansu na karbar akalla Naira 70,000 bayan cire duk wasu kudade.
Ma’aikatar ta ce duk wadanda aka samu ba su yi biyayya ga dokar ba, na iya fuskantar zaman gidan yari.
Gwamnatin na da nufin tabbatar da cewa duk wasu ma’aikata na karbar sabon mafi karancin albashi.
Sai dai Ƙungiyar EAPEAN ta nemi karin haske kan yadda albashin zai kasance bayan cire kudaden haraji da sauransu.
Shugabar Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya reshen Jihar Legas, ta nuna damuwarta game da yanayin tattalin arziki a kasar nan.
Ta ce ya zama dole, kamfanoni masu zaman kansu su fara biyan sabon mafi karancin albashi nan take.