Shahararriyar jaruma a Masana’antar Kannywood, wadda ta yi shura a masana’antar; Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa, akwai buƙatar duk wanda zai zama miji a gare ta; ya fara sanin wace ce ita? don gujewa abin da ka je ya dawo.
Jarumar, ta yi tashe matuƙa cikin ƙanƙanin lokaci; sakamakon yadda take sakin jiki ta yi rawa a duk lokacin da ta samu kanta a shirin fim.
- Masu Sha’awar Shiga Harkar Fim Su Shiga Da Zuciya Daya -Auwal Marafa
- Rahoto Ya Nuna Yadda Kanana Da Matsakaitan Kamfanonin Sin Ke Tafiya Cikin Tagomashi
A wani shiri da aka tattaunawa da Nafisan ta bayyana cewa, akwai buƙatar iyaye su fahimci cewa; tarbiyyar yara ya kansu ba kawai a bar uwa da xawainiyar tarbiyyar yaran kaxai ba, sannan kamata ya yi uba ya xauki kashi 50 na tarbiyyar yaransa; haka nan ita ma uwa ta xauki kashi 50.
Har ila yau, jarumar wadda ta fito a manyan fina-finan Hausa a Arewa da kuma na Kudancin wannan ƙasa ta bayyana cewa, duk da wasu na kallon ta a matsayin wata abar koyi a wajensu, amma fa hakan ba zai tilasta mata riƙa yin abin da lallai sai ya burge su ba.
“Kasancewata abar koyi a wajen waxansu mutane, musamman mata; ba zai zai sa na tauye kaina wajen riƙa yin abin da ba shi ne ra’ayina ba, domin kuwa ni ba ni da wani wanda nake kallo a matsayin abin kwaikwayo a wajena; don haka ni ban tilasta wa kowa yin koyi da ni ba, kowa ya je ya yi nasa ra’ayin”.
Har ila yau, ta ƙara da cewa; “Rayuwa sauƙi ne da ita, sannan kuma al’ada na iya canzawa a kowane lokaci, xan’adam kuma tara yake bai cika goma ba; wani lokaci zai iya yin daidai, wani lokaci kuma ya yi kuskure. Saboda haka, idan na ce kowane lokaci a yi koyi da abin da nake yi; akwai yiwuwar wasu su tsinci kansu wajen aikata ba daidai ba, wanda ni kuma ba zan so hakan ba”, in ji Nafisa.