Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sha alwashin zakulo duk wadanda suke da hannu a rikincin da ya barke a garin Mararraba Udege da kauyen Oduh a makon da ya gabata.
Ya ce, “hakkin Gwamnati ne ta samar da zaman lafiya da kare dukiyoyin al’umma, don haka, duk wanda aka samu da hannu a wannan rikicin za a mika shi gaban kotu ta yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata.
- ‘Yansanda Sun Cafke Baƙin Haure 165, An Miƙa Wa Hukumar NIS A Kebbi
- Kuɗin Fansa ₦13m, Kasonsa ₦200,000: Ɗan Shekara 50 Ya Jagoranci Garkuwa Da Ɗansa Da Iyalansa
“Abin bakin ciki ne mutanen da suke ‘yan kabila daya, Asali daya, Uwa daya, Uba daya amma suna kashe junansu saboda son zuciya da kwadayin abin Duniya.
“Wannan jahilci ne, babu yadda mai hankali zai yarda ya kashe dan uwanshi saboda abin duniya.
“Babu wata kabila da ake kira Afon dutsi ko Afon kasa. Duk sunansu AFO. Ya kuma janyo hankalin matasa da su daina yarda ‘yan siyasa batagari na amfani da su wajen neman biyan bukatar kansu, suna sanya su kashe junansu ko kona gidajen al’umma.”
Gwamna Abdullahi Sule ya kara da cewa, ya je kasar Sin don tattaunawa da kamfanin hakar Ma’adanai na ‘Juling Lithium Nasarawa Lithium Project’ a birnin Beijing, don ganin yadda kamfanin zai sake habaka basirar ma’aikata Leburori da ke aiki a kamfanin da ke Udege. Ganin cewa, ma’aikatan fiye da shekaru 20, aikin leburanci kawai suke yi babu ci gaba, don haka, dole a samu sauyi.
“Na tattauna da manyan Shugabannin kamfanin Shneyen. Nace sama da shekara 20 kuna hakar ma’adinan Tantalaye a Udege kuna tafiya da shi. Amma mutanen Udege baya ga aikin leburanci babu wani aikin da kuka basu. saboda haka, yanzu me zaku yi Wanda matasan gurin zasu samu aikin yi? Wannan maganar ta tabasu sosai. Nan take suka ce, za su gina katafaren kamfani da za a dauki matasa aiki a koyar dasu ilimin yadda ake sarrafa Ma’adinai da sauransu.
“Don haka, bai dace a kawo hargitsin da zai yi sanadin kulle wannan kamfani da wannan alherin da ke shirin zuwa wannan yankin ba, saboda banbancin siyasa.”
Shima a nasa jawabin OSu- Ajiris na Udege Mbeki Dr. Alhaji Halilu Bala ya yi godiya ga Gwamna Abdullahi Sule da ya yi tattaki da tawagarsa yazo ya gane wa idanunsa kuma ya dauki matakin da ya dace.
Sarkin yayi kira ga wadanda aka yi wa barna da su kara hakuri, doka za ta yi aiki kan duk wanda aka kama da hannu kan tayar da rikicin.