Gwamnatin Nijeriya, ta ce, duniya na bukatar karin matasa masu ilimin fasaha domin shawo kan tulin matsaloli da duniya ke fuskanta.
Ta ce, Nijeriya a matsayinta na kasa, ita kanta tana gayar bukatar wasu mata masu ilimin fasaha mai zurfi ta yadda za su taimaka su bayar da nasu gudunmawar wajen nausa cigaban kasar zuwa mataki na gaba.
- ‘Yansanda Sun Gargadi NNPP Da APC Kan Shiga Zanga-zanga A Kano
- Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Daliban Borno Gida Bayan Kammala Karatunsu A Kano
Ministan sadarwa, kere-kere da tattalin arzikin zamani, Dakta Bosun Tijani, shi ne ya shaida hakan a bikin daliban jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Akure a ranar makon jiya.
Ministan ya kara da cewa, domin Nijeriya ta samu ci gaba da bunkasa, akwai bukatar bunkasa bangarori guda uku da suka hada da na noma, masana’antu da kuma ayyuka wadanda aka yi amfani da su wajen auna manya-manyan kayan da ake samarwa a cikin gida tun 1980.
A cewarsa, wadannan bangarorin da saura ma, suna bukatar amfani da fasaha domin ganin an kyautatasu an kuma inganta su domin kawo ci gaban da ake fata.
Ministan wanda ya gabatar da lakca kan ilimi, bincike da a matsayin asasin cigaban tattalin arziki, ya ce, jami’o’in fasaha dole ne su tashi tsaye wajen shawo kan matsalolin da bangaren fasaha ke fuskanta a cikin kasar nan.
Tijani ya kara da cewa dole ne kuma jami’o’in su kasance masu kirkirar yanayin ayyuka ta hanyar amfani da fasaha, ya kuma hori dalibai da su kasance masu rungumar sana’ar tsayuwa da kafafunsu domin cigaba mai ma’ana.
Sai ya hori wadanda aka yayen da su cigaba da maida hankali wajen nuna halaye na kwarai a rayuwarsu na gaba, ya nemi su kara zurfafa tunaninsu kan fasaha domin cigaban kansu da na kasar nan.