Majalisar Dokokin ECOWAS, ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattaunawa da shugabannin ƙasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka fice daga ƙungiyar, tare da ƙoƙarin magance matsalolin siyasa a yankin Yammacin Afirka.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, wanda mamba ne a Majalisar ECOWAS, ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.
- Gwamna Lawal Ya Yaba Da Yadda Aikin Filin Jirgin Saman Zamfara Ke Tafiya
- Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio
Ya ce an yanke wannan shawara ne bayan wani taro da aka gudanar a Legas.
A cewar Sanata Barau, manufar kwamitin ita ce tattaunawa da shugabannin ƙasashen AES don fahimtar juna da jaddada muhimmancin ci gaba da kasancewa cikin ECOWAS, musamman idan aka yi la’akari da dangantakar tattalin arziƙi da zamantakewa da ke tsakanin jama’ar yankin.
Shugabar Majalisar Dokokin ECOWAS, Hadja Memounatou Ibrahima, ta ce kafa kwamitin zai taimaka wajen shawo kan matsalolin siyasa a yankin da kuma hana ƙarin ƙasashen Yammacin Afirka ficewa daga ECOWAS.
A ranar 29 ga watan Janairu, 2025, ƙasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar – waɗanda suka haɗe a ƙarƙashin Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) – sun sanar da ficewarsu daga ECOWAS.
Duk da hakan, ECOWAS ta tabbatar da cewa babu wata matsala a ɓangaren sufuri da kasuwanci tsakanin ƙungiyar da ƙasashen AES, domin har yanzu ana ci gaba da hulɗa tsakanin al’ummomin yankin.
Hakazalika, ECOWAS ta bayyana cewa ƙofarta a bude ta ke ga ƙasashen idan har sun shirya komawa cikin ƙungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp