Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Alieu Touray, ya bayyana shirin da kungiyar ke yi na kaddamar da rundunar soji mai jami’ai 260,000 domin yaki da ta’addanci a yankin Afirka.
Touray ya bayyana hakan ne a wajen taron hafsoshin tsaro na kasashen Afirka na 2025 mai taken: “Yaki da barazanar da ake fuskanta a wannan zamani ga zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka: rawar da hadin gwiwar tsaro za ta haifar” wanda aka yi ranar Litinin a Abuja.
- Beijing Zai Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani A Wuraren Adana Kayan Tarihi
- Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta
Shugaban ECOWAS, wanda kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya wakilta, ya ce, kungiyar na bukatar dalar Amurka biliyan 2.5 don samar da kayan aiki da kuma tallafin kudi ga sojojin da za a tura kasashen da ke fama da ‘yan ta’adda.
LEADERSHIP ta bayar da rahoton cewa, kasashe 36, daga cikin kasashe 54 na Afirka ne suka halarci taron.
Yayin da wakilin Jamhuriyar Nijar ya yi na’am da wannan shirin amma, Mali da Burkina Faso ba su halarci taron ba wanda watakila hakan ba zai rasa alaka da rikicin siyasa tsakanin kasashen Sahel da ECOWAS ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp