Babban Mataimakin Shugaba kuma Babban Editan Rukunin Jaridun LEADERSHIP, Azu Ishiekwene, ya lashe kyautar gwarzon shekara a fannin rubutu a shafin Jaridu.
Gasar ta bana ita ce karo na 30 na bikin bayar da lambar yabo ta Nigerian Media Merit Award (NMMA) 2022, wanda aka gudanar a Legas ranar Lahadi.
- Oramah, Marwa, Amusan Sun Yi Nasarar Zama Gwarazan Kamfanin LEADERSHIP A 2022
- Wakilin Jaridar LEADERSHIP Ya Maka Ado Doguwa A Kotu Kan Yi Masa Mahangurba
Mista Ishiekwene, wanda aka fi sani da Azu, ya doke Abimbola Adelakun da Tunde Odesola dukkansu daga Jaridar PUNCH.
NMMA tana karkashin jagorancin tsohon shugaban kamfanin Lintas, Mista Dele Adetiba. Kyautar a wannan rukunin ana kiranta da Alade Odunewu, daya daga cikin gwarzayen da suka yi fice a tarihin Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da LEADERSHIP ta fitar mai dauke da sa hannun Manajan Editan Raliat Ahmed-Yusuf, jaridar ta ce, “Karramawar ta sake nuna irin kwazo da sharhi mai ingancin na, Mista Azu, wanda ya dauki tsawon shekaru yana yi a fannin rubutu.
Azu, wanda ya lashe wannan lambar yabo ta NMMA a kalla sau hudu a baya a cikin shekaru goma uku da rabi, ya samu lambar yabo ta farko a aikin jarida shekaru 34 da suka wuce lokacin da ya ci lambar yabo ta Babatunde Jose ta dalibin mafi kwazo da zalaka wajen buga takardu a Sashen Sadarwa na Jami’ar, Legas.
Babban Editan na ɗaya daga cikin ‘ƴan jaridun Nijeriya da suke da kwazon rubutu a shafukan Jaridu da ake wallafawa a kasashen Ghana, Argentina, Afirka ta Kudu, Turai da Amurka.