• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

EFCC Na Binciken Gwamnan Zamfara Kan Almundahanar Biliyan 70

by Sadiq
2 years ago
EFCC

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), ta ce gwamnan Jihar Zamfara mai barin gado, Bello Matawalle na fuskantar bincike kan zargin almundahanar Naira biliyan 70.

Hukumar, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ana binciken gwamnan na APC kan zargin cin hanci da rashawa, bayar da kwangiloli da kuma karkatar da sama da Naira biliyan 70.

  • Mutum 2 Sun Shiga Hannu Kan Kisan Ma’aikatan Ofishin Jakadancin Amurka
  • Na Yi Mamakin Ganawar Antony Blinken Da Tinubu -Atiku

“Kudaden da aka samo a matsayin lamuni daga tsohon bankin da ake zargin don gudanar da ayyuka a fadin kananan hukumomin jihar, ana zargin gwamnan ne ya karkatar da su ta hanyar wasu ‘yan kwangila wadanda suka karbi kudin kwangilar da ba a aiwatar da su ba.”

“Binciken da Hukumar ta gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa sama da kamfanoni 100 ne suka karbi kudaden, ba tare da wata shaida ta hidimar da aka yi wa jihar ba.”

EFCC ta ce an gayyaci wasu daga cikin ‘yan kwangilar tare da yi musu tambayoyi, inda ta kara da cewa “sun bayyana bayanai kan yadda ake zargin gwamnan ya tilasta musu mayar masa da kudaden da suka karba daga asusun gwamnati ta hannun mukarrabansa bayan sun mayar da su Dalar Amurka”.

LABARAI MASU NASABA

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

“Sun tabbatar da cewa ba su yi wa jihar Zamfara wani aiki ba amma an ce an umarce su da su mayar da kudaden da aka biya su dalar Amurka su koma hannun gwamnan jihar ta hannun wasu kwamishinoninsa, musamman kwamishinonin da ke kula da harkokin kudi da kananan hukumomi.”

“A ci gaba da bincike kan bada kwangilar da gwamnatin Matawalle ke yi, musamman na ayyuka a kananan hukumomi, hukumar ta kwato kudi Naira miliyan 300 daga wani kamfani mai suna Fezel Nigeria Limited. An gano kudaden ne zuwa kamfanin Zamafara Investment Company.

“A Nijeriya gwamnoni da mataimakansu na da kariya daga fuskantar tuhuma yayin da suke kan mulki, dalilin da ya sa har yanzu EFCC ba ta kama Gwamna Matawalle ba ke nan.”

Matawalle, wanda ya sha kaye a zaben gwamnan jihar na 2023 a watan Maris, zai kammala wa’adin mulkinsa na shekara hudu a ranar 29 ga wata Mayu, 2023.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru
Wasanni

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL
Manyan Labarai

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
Next Post
NNPP Ba Ta Da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu A Kotu –Buba Galadima

NNPP Ba Ta Da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu A Kotu –Buba Galadima

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.