Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta kama mutane 15 da ake zargi da aikata zamba ta yanar gizo a babban birnin tarayya Abuja.
Jami’an hukumar EFCC ta Makurdi, ne suka cafke waɗanda ake zargin yayin wani samame a Amax Apartment da ke unguwar Guzape, bayan samun sahihan bayanai da ke danganta su da ayyukan damfara ta intanet.
- Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Hanyar Abuja Zuwa Keffi
- AU Ta Zabi Sabbin Shugabanni Ana Tsaka Da Tashe-tashen Hankula A Nahiyar
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na ‘X’ a ranar Talata, EFCC ta bayyana cewa an ƙwato kayayyaki da dama daga hannun su, ciki har da mota ƙirar Toyota Highlander, mai lambar rajista ta musamman (BORNO AAA) da kuma wayoyin salula da dama.
EFCC ta ce waɗanda ake zargin sun bayar da bayanai masu amfani, kuma za a gurfanar da su a kotu domin girbar abinda suka shuka da zarar an kammala bincike.
Hukumar ta sha alwashin ci gaba da fafutuka a kan masu aikata laifukan zamba ta yanar gizo a faɗin Nijeriya, domin rage yawaitar ayyukan damfara da sauran laifukan da suka shafi intanet.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp