Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kama Umar Isa, tsohon babban jami’in kuɗi na kamfanin mai na Nijeriya (NNPCL), kan zargin satar dala biliyan 7.2 da aka kashe wajen gyara matatun mai na Kaduna, Warri da Fatakwal.
Bayanai daga hukumar sun nuna cewa an kama Isa da Jimoh Olasunkanmi, tsohon manajan darakta na matatar mai ta Warri, a birnin Abuja. Ana ci gaba da binciken manyan tsoffin jami’an da ke da hannu a lamarin.
- EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Kamfanoni Biyu Gaban Kuliya Bisa Damfarar Naira Miliyan 80
- NNPC Ya Ƙara Kuɗin Fetur, Duba Sabon Farashin
Masu binciken EFCC sun mayar da hankali kan zarge-zargen cin hanci, da zambar kuɗaɗen jama’a, da kuma karɓar cin hanci daga kwangila. A lokacin da Isa yake aiki a matsayin CFO, shi ne ke kula da raba kuɗaɗen da aka ware wa gyaran matatun.
Kwamitin majalisar dattijai kan bibiyar kuɗin jama’a a ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada, ya nuna damuwa game da rashin daidaiton bayanan kuɗi na NNPC daga 2017 zuwa 2023.
“Abubuwan da muka gano a cikin lissafin NNPC sun fi ban tsoro. Muna magana ne kan tiriliyoyin Naira da babu wani bayanin su,” in ji Sanata Wadada.
Kwamitin majalisa ya ba NNPC kwanaki bakwai don ta ba da cikakken bayani kan batutuwan da aka bankaɗo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp