Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta kama wasu ‘yan China huɗu da wasu ‘yan Nijeriya 27 bisa zargin haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Jos, babban birnin Jihar Filato.
Mai magana da yawun hukumar EFCC Dele Oyewale, ne ya shaida haka cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata a Abuja, inda ya bayyana cewa an kama mutanen ne a ranar Asabar, a harabar kamfanin Jiasheng Nigeria Limited, da ke Dura Du na anguwar Rayfield, kan hanyar Mangu a Jos.
- Kamfanin Kasar Sin Zai Gudanar Da Aikin Farfado Da Muhallin Halittu Na Kogin Nairobi Na Kasar Kenya
- El-Rufai Ya Yi Alƙawarin Haɗa Abokan Hamayya Don Yaƙar APC A Zaɓen 2027
Oyewale, ya ce an kama su ne bayan samun sahihan bayanan sirri da ke danganta kamfanin da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar.
Ya kara da cewa an samu wasu kayayyaki a wurin, ciki har da babbar motar dakon kaya ɗauke da buhuna takwas na ‘Monazite’ da aka sarrafa, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 1000, wanda darajar kowanne buhu ta kai naira miliyan hudu, da kuma wasu ma’adinai da ba a sarrafa ba da ake zargin an haƙo su ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu domin su fuskanci hukunci.
Idan ba a manta ba a kwanaki kaɗan da suka wuce gwamnatin Jihar Filato, ta sanar da sanya haramci kan harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar saboda wasu dalilai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp