Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta saki Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Rt. Hon Olakunle Oluomo, daga tsarewar da ta yi masa.
An saki Oluomo ne a ranar Juma’a bayan shafe tsawon dare guda a ofishin EFCC da ke Abuja bisa zarginsa da sama da fadi da karkatar da kudade.
- EFCC Ta Cafke Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ogun
- EFCC Da NIS Za Su Yi Hadin Guiwa Kan Yaki Da Cin Hanci
Da yake tabbatar da sakin Oluomo ga LEADERSHIP, Hadimin Kakakin a fannin yada labarai, Mallam AbdulGhaffar Adeleye, ya ce, Mai gidan nasa ya samu ‘yancinsa yanzu haka yana gida, “Jama’a su yi watsi da jita-jitar cewa an dauke shi zuwa Abuja domin tambayoyi.” Cewarsa.
LEADERSHIP ta labarto cewa Oluomo dai ya shiga hannun EFCC ne a ranar Alhamis da safiya a filin Jirgin saman Legas bayan zargin da aka masa na kin amsa gayyatar da hukumar ta sha masa domin amsa tambayoyi.