• English
  • Business News
Thursday, September 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

El-Rufai Ya Zargi Bangaren Shari’a Da Cin Hanci Da Rashawa

by Khalid Idris Doya
4 months ago
in Labarai
0
Nijeriya Ba Za Ta Taba Maimaita Yakin Basasa Na Shekarar 1967 —el-Rufai
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi bangaren shari’a ta Nijeriya da rashawa, inda ya yi zargin cewa alkalai da lauyoyi da amsar na goro, inda ya ce suna cin amanar aikinsu a yayin da suke shari’a.

Ya shaida hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin makon shari’a, wanda reshen kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) a Bwari da ke Abuja ta shirya, El-Rufai ya ce yanzu ‘yan Nijeriya sun yanke aminci da yarda da suke yi da sashin shari’a sakamakon jinkirin da ake samu na tabbatar da adalci da shigar da son zuciya na kashin kai a maimakon muradin jama’a.

  • Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 
  • Ingancin Tattalin Arzikin Sin Mai Bude Kofa Na Bayyana Sosai Duba Da Yawan Zuwan Baki Masu Sayayya

“Haka zalika, bangaren shari’armu, wanda ya kamata ya zama ginshikin wanzar da gaskiya da oda, amma yana fama da matsalolin da suke bukatar a duba. Damuwar da aka samu game da jinkirin shari’a, rashin ingancin tsarin aiki, da kuma wasu lokuta cin amanar shari’a, suna zubar da kwarin gwiwar jama’a,” in ji shi.

Tsohon gwamnan ya koka kan yadda ake yawan samun umarnin kotu na dakatar da ci gaba da shari’a ko kama kan wasu lamuran da suka shafi siyasa, inda ya zargi wasu ma’aikatan shari’a da amfani da tsarin kotuna domin cimma muradi ta siyasa.

Ya kuma sake nuna damuwa kan yadda ake samun rashin daidaito a bangaren shari’a da adalci a fadin kasar nan, yana mai nuna cewa bangaren shari’a ya zama dandalin kare muradun gwamnati mai ci wanda kuma ba hakan ya kamata ba.

Labarai Masu Nasaba

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

El-Rufai ya yi kira ga alkalai da lauyoyi da su ji tsoron Allah su koma kan asalin aikin da ke gabansu tare da himmatuwa wajen wanzar da adalci da gaskiya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: El-Rufai
ShareTweetSendShare
Previous Post

GORON JUMA’A

Next Post

Gwamnan Kano Ya Ceto Dalibai 84 Da Ganduje Yaki Biya Wa Kudin Makaranta A Cyprus

Related

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 
Labarai

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

46 minutes ago
Boko Haram Na Yin TikTok, Suna Sarrafa Jirage Marasa Matuƙi Don Sa Ido Kan Sansanonin Soji – Bulama 
Labarai

Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

2 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

4 hours ago
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja
Labarai

Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 10 A Jihar Neja

7 hours ago
DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci
Manyan Labarai

DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci

9 hours ago
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi
Labarai

‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata

10 hours ago
Next Post
Gwamnan Kano Ya Ceto Dalibai 84 Da Ganduje Yaki Biya Wa Kudin Makaranta A Cyprus

Gwamnan Kano Ya Ceto Dalibai 84 Da Ganduje Yaki Biya Wa Kudin Makaranta A Cyprus

LABARAI MASU NASABA

An Zabi Wuraren Ban Ruwa Hudu Na Kasar Sin Domin Shigar Da Su Jadawalin Wuraren Ban Ruwa Na Kasa Da Kasa

An Zabi Wuraren Ban Ruwa Hudu Na Kasar Sin Domin Shigar Da Su Jadawalin Wuraren Ban Ruwa Na Kasa Da Kasa

September 11, 2025
Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

September 11, 2025
Shawarar Jagorantar Harkokin Duniya: Mafitar Sin Ga Kasa Da Kasa

Shawarar Jagorantar Harkokin Duniya: Mafitar Sin Ga Kasa Da Kasa

September 11, 2025
Boko Haram Na Yin TikTok, Suna Sarrafa Jirage Marasa Matuƙi Don Sa Ido Kan Sansanonin Soji – Bulama 

Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

September 11, 2025
Wata Mahanga Ta Daban Na Kallon Ayyukan Ta’addanci

Wata Mahanga Ta Daban Na Kallon Ayyukan Ta’addanci

September 11, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

September 11, 2025
Najeriya: Ajandar Jagorantar Duniya Ta Ba Da Gudummawa Ga Tsarin Kasashen Duniya

Najeriya: Ajandar Jagorantar Duniya Ta Ba Da Gudummawa Ga Tsarin Kasashen Duniya

September 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

Cutar Diphtheria Ta Kashe Yara 10 A Jihar Neja

September 11, 2025
DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci

DSS Ta Gurfanar Da Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Kan Zargin Ta’addanci

September 11, 2025
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi

‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata

September 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.