Daya daga cikin kakakin yakin neman zaben Atiku a zaben 2023, Barista Daniel Bwala, ya ce gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai koma jam’iyyar PDP kafin zaben 2023.
Bwala, wanda ya yi wannan ikirarin a ranar Litinin a shafin sa na Twitter, yayin maida martani ga gwamna elrufa’i wanda yake keketa dariya kan wani sharhi da aka yiwa Bwala karkashin wani faifan Bidiyo da aka wallafa.
Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne Bwala wanda maitaimaka wa mataimakin shugaban majalisar dattawa ne, Ovie Omo-Agege, ya ajiye mukaminsa ne ya koma jam’iyyar PDP daga jam’iyyar APC don nuna rashin amincewarsa da zabin Tikitin musulmi da musulmi a zaben shugaban kasa.
A lokacin da yake APC, Bwala ya yi fira a gidan talabijin da dama inda yake kakkausar suka ga jam’iyyar adawa ta PDP, sabuwar jam’iyyarsa.
A makon da ya gabata ne aka nada Bwala tare da fitaccen tsohon dan majalisar tarayya Sanata Dino Melaye a matsayin mai magana da yawun yakin neman zaben Atiku na zaben 2023.
Kakakin yakin neman zaben Atiku, Bwala ya ce ba zai yi cece-kuce da gwamnan jihar Kaduna ba, domin nan gaba kadan zai komo Jam’iyyar Adawa ta PDP kafin 2023.