A ranar Alhamis ne tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya gurfana a gaban kotu inda ya bukaci a canza masa sharudan belinsa. Emefiele na neman a sake duba wasu Sharuɗan da ke cikin kundin Sharuɗan belinsa.
Yanzu haka dai Emefiele yana fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume shida da suka shafi zamba cikin aminci ta ɗimbin kuɗaɗe waɗanda suka kai kimanin Naira Naira biliyan 1.2.
- Ba Wanda Zai Iya Kawo Tsaiko Ga Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
- Ba Kwashe Kudin Al’umma Ya Kawo Mu Zamfara Ba – Gwamna Dauda
An sake shi daga gidan gyaran hali na Kuje wanda tun farko anan aka tsare shi a ranar 23 ga Disamba, 2023, kwanaki 34 bayan da alkali ya bayar da belinsa.
A yanzu haka mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya yana sauraren hujjoji kan lamarin, kuma nan ba da jimawa ba za a yi karin bayani.
Akwai karin bayani nan gaba kadan…