Gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele ya nemi gafara kan kalubalen da aka fuskanta kan tsarin hada-hadar kudi ta Internet.
Emefiele ya nemi gafarar ne a taron kwamitin tsarin kudi na MPC da aka gudanar a ranar Talata a Abuja, inda gwamnan ya aminta da cewa, an samu kalubalen wanda a yanzu, an warware kalubalen.
- Zaben 2023: Atiku Da Obi Sun Shigar Da Kara Ta Kalubalantar Nasarar Tinubu
- Xi Da Putin Sun Jaddada Tattaunawa A Matsayin Mafita Ga Rikicin Ukraine
Da yake amsa tambayoyi akan abin da ya shafi bankuna ganin yadda wasu bankuna a kasar Amurka ke durkusewa, gwamnan ya ce bankuna a kasar nan ba za su durkushe ba kamar yadda aka samu a kasar Amurka ba.
Emefiele ya bayar da tabbacin cewa, daukacin bankuna a kasar nan, za su ci gaba da samun kariyar da ta kamata.
A cewar Emefiele, babu wani mai ajiya a bankunan da ke kasar nan da zai yi asarar kudin da ya ajiye tun daga shekarar 2000, inda ya ce, an samu wannan nasarar ne, saboda kyakyawan tsarin da bankin Nijeriya ya samar, mussaman don kare kudaden masu ajiya a bankunan.
Emefiele ya kuma gargadi masu ruwa da tsaki a fannin tafiyar da bankuna a kasar nan, da su kwana da sanin cewa, lasisin kafa bankuna da ake ba su dama ce bai wai dole ba ne wanda kuma za a iya karbewa idan aka aikata ba daidai ba.
A karshen taron na MPC, mahalarta taron sun amince da a kara kudin haraji zuwa kashi 18 daga wanda ake yi a baya na kashi 17 wanda aka amince a watan Janairu.