ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben 2023: Atiku Da Obi Sun Shigar Da Kara Ta Kalubalantar Nasarar Tinubu

by Sadiq
3 years ago
Zaben 2023

Jagororin manyan jami’iyyun adawa biyu; PDP da LP, sun shigar da kara a kan neman soke sakamakon zaben shugaban kasa na watan Fabrairu da suke kalubalanta, kamar yadda takardun kotu suka nuna, domin fara wata shari’ar da ka iya daukar tsawon watanni.

An shigar da kararraki da dama na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar Nijeriya, amma ga dukkan alamu babu wadda ta yi nasara.

  • NIS Reshen Ribas Ta Kafa Kwamitin Bunkasa Walwalar Jami’ai
  • Zaben 2023 Ya Nuna Dimokuradiyyar Nijeriya Ta Bunkasa -Buhari

Dan takarar babbar jami’iyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na jami’iyar Labour Party, sun roki kotun daukaka kara da ta soke zaben da Bola Tinubu dan takarar jami’iyar APC ya lashe.

ADVERTISEMENT

Shugabannin jami’iyyun adawan sun fada a wata takardar rantsuwar kotu cewa zaben na tattare da magudi kana sun zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da take doka, inda ta gaza amfani da na’urar lantarki wajen daukar sakamakon zabe daga runfunan zabe da ma wasu zargi zargin.

Atiku da Obi sun nemi umarnin kotu kan sako bayanan zaben shugaban kasa, kana INEC ta gudanar da sabon zabe.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Tinubu ya kare zaben da cewa an gudanar da shi cikin adalci.

Obi da ya shigo takara a karon farko, ya samu goyon bayan matasa da sababbin masu kada kuri’a kuma da alamar ya fadada takarar, inda ya bai wa masu zabe kwarin gwiwar samun sauyi daga shekaru na wahala da tashin hankali karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari mai shekaru 80, tsohon Janar na soja.

Amma Obi ya zo na uku bayan Tinubu da Atiku, wanda dukkaninsu nada jami’iyyu siyasa masu karfi da kuma gomman shekaru na harkokin siyasa.

APC da PDP sune suka gudanar da mulkin Najeriya tsakaninsu tun bayan karshen mulkin soja a shekarar 1999.

Masu sa ido a kan zaben sun zargi INEC da rashin cikakken shiri da kuma jinkiri wurin fara zabe amma basu yi zargin tafka magudi ba. Hukumar kanta ta roki gafara a kan matsalolin na’ura da ta fuskanta wurin kidaya.

Kotun daukaka karar tana da kwanaki 180 ta saurari karar kana ta zartar da hukunci a karar da Obi ya shigar ta kalubalantar sakamakon.

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Emefiele Ya Roki Gafarar ‘Yan Nijeriya Kan Matsalar Hada-Hadar Kudi Ta Intanet

Emefiele Ya Roki Gafarar 'Yan Nijeriya Kan Matsalar Hada-Hadar Kudi Ta Intanet

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.