• English
  • Business News
Sunday, August 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Etsu Nupe Ya Jaddada Buƙatar Sama Wa Sarakunan Gargajiya Gurbi A Tsarin Mulki

by Rabi'u Ali Indabawa
15 hours ago
in Labarai
0
Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mai Martaba, Etsu Nupe na 13, wanda ya shafe shekaru 22 a kan karagar mulki. Janar ɗin soja mai ritaya, Alhaji (Dr) Yahaya Abubakar, a wannan tattaunawa da ya yi da manema labarai ya bayyana dalilin da ya sa ya kamata a bai wa sarakunan gargajiya ayyukan da kundin tsarin mulki ya tanada da kuma alfanun da ke tattare da samun wadanda suka yi aikin soja a cibiyoyin gargajiya, da dai sauran batutuwa kamar almajirai da ƴansandan jiha.

Ya ce, “Muna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bamu lokaci da rayuwa da kuma ikon riƙe wannan kujera ta magabata. Mun hau wannan kujera a ranar 11 ga Satumbar 2003; bayan mun yi aikin soja sama da shekara 30: Allah ya ƙaddara muka maye wannan gurbi. Tsawon shekaru 22 ina kan wannan karaga. Na yi iya ƙoƙari na wajen ganin mun yi duk abin da za mu iya yi wa mutanenmu, mene ne burin mutane; jin daɗinsu; tsaro; da haɗin kan mutanenmu, musamman Nufawa.”

“Nufawa na daya daga cikin manyan ƙabilu a Nijeriya. Kuma mun watsu a ko’ina a Arewa, Kudu, Gabas da Yamma, har ma da ƙasashen waje.

  • Tattaunawa Da Mai Martaba Etsu Nupe Kan Bikin Cikarsa Shekara 20 A Karaga
  • Addu’a Ce Mafita Kan Matsalar Tsaron Nijeriya – Etsu Nupe

ɗon haka, muna son ganin yadda za mu samu hada kan al’umma, da jiha, da Nijeriya baki daya,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa; “Mun fara da kyakkyawan tushe; inda muka assasa wani taron da aka fi sani da Ranar Nufawa’ (Nupe day), bikin da muke yi a kowace shekara ranar 26 ga Yuni. Idan mun koma tarihi, zuwa yaushe ne turawa suka yi mana mulkin mallaka daga Kudu zuwa Arewa.? Kakanninmu sun nemi su yaƙe su ba tare da tsoro ba, amma aka yi asarar rayuka domin sadaukarwa. ɗon haka, muna girmama wannan ranar a matsayin ranar nasara, Mun ware ranar 26 ga watan Yuni domin yin wannan bikin.”

Labarai Masu Nasaba

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM

Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

“Kazalika sarkin ya bayyana cewa, mun kuma duba yanayinmu. Me muke da shi? Me za mu iya yi? Me ya kamata mu yi domin inganta rayuwar mutanenmu? Allah ya albarkaci ƙasarmu, ƙasa ce mai faɗi sosai, kuma ta dace da ayyukan noma.

Mun kuma yi la’akari da fannin ilimi. Jihar Neja, an san tana gaba a fannin ilimi. To, kwatsam, sai wannan mataki ya samu tasgaro, yara ba su iya cin jarabawar WASC, zuwa makaranta ya yi ƙasa da ƙasa, ba a kula da malamai yadda ya kamata. Wasu makarantun ba su da malamai. Za ka ga makaranta mai yawan dalibai 300 tana da malami daya ko biyu, hakan ba abu ne mai yiwuwa ba,”in ji shi.

Ya ci gaba da cewa “ɗon haka muka yanke shawarar shiga wannan fannin ilimi ta hanyar kafa makarantar firamare, sakandare, kuma Allah cikin rahamarSa, muna kafa jami’a a yanzu, wacce aka fi sani da Jami’ar Edusoko, don ƙarfafawa da kuma ci gaba da abin da gwamnati ke yi, domin mun yi imanin cewa shirye-shirye da ayyuka a cikin gwamnati ba za su iya biyan bukatun jama’a ba, kuma muna buƙatar cim ma ƙoƙarinmu.

Kazalika fannin lafiya ba mu yi sake da shi ba. Mun yanke shawarar ƙarfafa wa mutanenmu da su je neman lafiya, duba lafiyarsu a asibitoci, sannan kuma mun samu damar tattara kayan aiki don gina cibiyar kiwon lafiya inda masu ƙaramin ƙarfi za su iya zuwa. Jama’a za su je a ba su magungunan, wadanda bai da shi, mun rubuta ka je ka saya. ɗon haka, muna taimakawa a wannan ɓangare.

Sannan ya ce, “Mun gayyato wata ƙungiya mai zaman kanta, daga ƙasar Amurka, da ta zo ta yi wa jama’armu magani, masu larurar ciwon ido kyauta, da masu larurar ciwon kunne.”

da ya taɓo ɓangaren tsaro kuwa, cewa ya yi, abu ne da yake da matuƙar muhimmanci. Ku sani, shi tsaro haƙƙin kowa ne. Ganin haka ya sa muka kafa kwamitin da zai kula da harkokin tsaron cikin gida a garin Bida domin a wani lokaci mun gano cewa muna da ɗimbin matasa da ba su da aiki; wasu matasa suna shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, suna kan tituna ko kusurwoyin tituna, suna takurawa mutane, mata, musamman, da kuma mutane marasa gata. An hana fita da ƙarfe shida; dole ne ku zauna a cikin gida, in ba haka ba, za a ci zarafinku ko wani abu makamancin wannan. ɗon haka sai da muka kafa wannan kwamiti domin kula da hakan. Wannan kwamitin yana fara aiki wannan barazanar ta fara raguwa.

Batun Tsofaffin shugabanin ƙasa kuwa cewa ya yi, wadannan shugabanni da muke da su kuwa, suna da amfani gare mu, domin a yanzu suna martaba, domin wasu mutane daga wasu wurare da suke zuwa neman shawara, goyon baya da mafita ga matsalolin da suke da su. ɗon haka, sun zama abin da kuke kira gumaka, wuraren bincike, inda mutanen da ba su ma son zuwa Neja za su zo daga Arewa, Kudu, Gabas, Yamma, don ganin wadannan mutane.”

da yake magana kan dangantakarsa da sarakunan gargajiya da kuma tsofaffin sojoji kamar sarkin Musulmi, cewa ya yi, “Wannan haɗin gwiwa ce da muka samu daga sojoji mai ƙarfin gaske, hakan na motsa mu a cikin sabon aikinmu na shugabannin gargajiya da na addini.”

A ɓangaren rawar da sarakunan gargajiya ke takawa kuwa, cewa ya yi, “ Ina ganin kuskure ne a cire aikin sarakuna ko cibiyoyinsu daga kundin tsarin mulkin 1999. Kuskure ne. In ba haka ba, idan ka duba duk kundin tsarin mulkin da muke da shi, kafin samun ƴancin kai, lokacin ƴancin kai, har zuwa 1979, akwai ayyuka na cibiyoyin gargajiya.

“Amma, Allah ya san abin da ya faru, ba zato ba tsammani kwatsam an cire su. Kuma a lokacin da aka cire ɗin, akwai abin da kuke kira, taɓarɓarewar alaƙa, tsakanin gwamnati da masu mulki; an samu giɓi kuma giɓin ya yi yawa.”

Ya ci gaba cewa, “Wannan alaƙa da ta yanke. cibiyoyin gargajiya sun san abin da ake ji kuma su ne za su tilasta mutanensu sanin abin da ake so, sanin abin da suke yi, idan aka shigo da sarakuna su cikin harkokin siyasa, yanke shawara, da aiwatarwa, duk wadannan abubuwa za su yi kyau. Misali, idan za mu zauna kafada da kafada a majalisar jahohi da matakin tarayya, to manufofin ilimi, noma, kiwon lafiya da dai sauransu, idan gwamnati ta kawo abin da zai amfani al’ummarmu, to ko shakka babu za mu zartar da shi, kuma mu gamsar da al’ummarmu ba tare da tantama ba, cewa eh, wannan shirin yana da kyau a gare ku. Idan kuma gwamnati ta zo da wani abu da ba zai amfane su ba, tun daga sama a can za mu gaya wa gwamnati a’a, mutanenmu ba su saba da wannan ba, idan kuna so su yi amfani da shi, dole ne sai an bi al’adunmu na gida.”

“Wanio misalin, mu dauki batun allurar rigakafin cutar shan inna a lokaci guda, shirin ya zama wani abin tausayi, domin gwamnati ba ta sanya aikin a hannu kowa ba. ta yi gaban kanta ma’aikatanta suka tafi ƙauyuka don aiwatar da aiki, aka kore su, domin a ganinsu an zo a halaka su, a lalata musu mazaje, don haka suka nuna ba sa so. Gwamnati ta dauki lokaci mai tsawo a wannan yanayi, daga baya dole ne ta shigar da cibiyar gargajiya don shiga tsakani. Kuma a lokacin da muka shigo, mun sami damar wayar da kan jama’armu, kafin mu iya fahimtar da su ɗin, sai da muka dauki tawagar likitoci don tabbatar da gaskiyar wannan rigakafin,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “A lokacin da muka tabbatar da cewa yana da anfani ga jama’a kuma ba ya cutar da rayuwar dan’Adam, a nan muna da ikon zuwa mu gaya wa mutanenmu, a’a, a’a, a’a, kada ku damu, wannan abu bai saɓa wa kowace lafiya ba, hasali ma zai inganta lafiyar yaranmu ne, ana nufin yara tsakanin shekara daya zuwa biyar, za a yi musu kuma za su samu lafiya. ɗon haka, mun shawo kansu. A can kuma, sun fara yarda da shirin, sannan kuma a yanzu mun yi sa’a, Majalisar ɗokoki ta 10, suna aiki ba dare ba rana, don ganin an dawo da wannan cibiya a kan turba.”

Bugu da ƙara, akwai batun, kafa cibiyoyin kiwon lafiya a dukkan ƙananan hukumominmu, 774, an kashe maƙudan kuɗi, nan ma kawai sai suka tafi ƙauyuka, don kafa cibiyoyin kai tsaye. To ka gaya min, wadanne likitocin da ke zaune a cikin birni ne za su je ƙauyukan da babu ruwa, babu haske wuta, babu ma hanyoyi kuma a ce za su yi wannan aikin?”

“da a ce an shigo da mu domin bayar da shawara, da sai mu ce a maimakon a yi dukkan ƙananan hukumomi 774, a rage su zuwa dari kacal, dari daya ko dari biyu kawai, za ku iya tsawaita su daga baya. Sannan kafin ku je ƙuyukan, ku tabbata, hanyar ƙauyen tana da kyau, ku tabbatar cewa ƙauyen yana da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ko wani abu makamncin haka, sanna ku tabbatar akwai ruwan sha mai kyau,” in ji shi.

da ya zo batun rasuwar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari cewa ya yi; “Mun yi imani Allah yana bayarwa kuma Allah yana karɓa, kuma dukkan rayuka daga Allah suke, kuma wajibi ne dukkan rayuka su koma gare shi. Allah ya jiƙansa, su kuma ƴan uwa na kusa, Allah ya ba su ƙwarin gwiwar jure wannan rashi mara misaltuwa, da ma al’ummar ƙasa baki daya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: NigerNupe
ShareTweetSendShare
Previous Post

Babban Bankin Sin Ya Yi Alkawarin Ba Da Goyon Baya Ga Kirkire-Kirkire Da Sayayya

Next Post

Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?

Related

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM
Labarai

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM

1 hour ago
Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto
Labarai

Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

18 hours ago
Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto
Labarai

Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto

19 hours ago
Ma’aikatan Jinya Sun Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu 
Da ɗumi-ɗuminsa

Ma’aikatan Jinya Sun Janye Yajin Aiki Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu 

20 hours ago
Gwamna Fintiri Ya Karrama Kocin Super Falcons, Madugu Da Naira Miliyan 50
Labarai

Gwamna Fintiri Ya Karrama Kocin Super Falcons, Madugu Da Naira Miliyan 50

21 hours ago
Kongo Na Neman Goyon Bayan Nijeriya Kan Shugabancin UNESCO
Manyan Labarai

Kongo Na Neman Goyon Bayan Nijeriya Kan Shugabancin UNESCO

21 hours ago
Next Post
Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?

Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?

LABARAI MASU NASABA

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM

Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM

August 3, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

August 3, 2025
Ban Yi Danasanin Shiga Harkar Fim Ba – Baba Ƙarami

Ban Yi Danasanin Shiga Harkar Fim Ba – Baba Ƙarami

August 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji

Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji

August 3, 2025
Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

August 3, 2025
Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

August 2, 2025
Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?

Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?

August 2, 2025
Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto

Etsu Nupe Ya Jaddada Buƙatar Sama Wa Sarakunan Gargajiya Gurbi A Tsarin Mulki

August 2, 2025
Babban Bankin Sin Ya Yi Alkawarin Ba Da Goyon Baya Ga Kirkire-Kirkire Da Sayayya

Babban Bankin Sin Ya Yi Alkawarin Ba Da Goyon Baya Ga Kirkire-Kirkire Da Sayayya

August 2, 2025
Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya

Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya

August 2, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.