Rahotanni daga ofishin kula da bashi na ƙasa (DMO), sun bayyana cewa bashin da ake bin Nijeriya ya ƙaru zuwa Naira tiriliyan 149.39.
Wannan na nufin an samu ƙarin Naira tiriliyan 27.72 idan aka kwatanta da tiriliyan 121.67 da aka samu a shekarar 2024.
- Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya
- Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
Wannan hauhawar bashi ya samo asali ne daga faɗuwar darajar Naira, wadda ke sa darajar bashin da Nijeriya ta karɓo daga waje ya ƙaru sosai.
A cewar DMO, daga cikin bashin da ake bin Nijeriya, tiriliyan 70.63 na waje ne wanda ya kai kusan dala biliyan 45.98.
A baya bashin wajen yana tiriliyan 56.02 (dala biliyan 42.12), wanda ke nuna cewa ya ƙaru sosai.
Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen.
Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond.
Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.76, kwatankwacin dala biliyan 51.26.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp