Kwamitin da ke kula da asusun ajiya na kasa, FAAC ya tara Naira Tiriliyan 1.594 A Watan Satumba, ya raba Naira Biliyan 903 Zuwa bangarorin Gwamnati Uku.
Kwamitin FAAC ya sanar da samun kudaden shiga na Naira tiriliyan 1,594,763 daga watan Satumban 2023. Wannan shi ne karo na biyu da gwamnati ke samun karin kudaden shiga tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayu.
FAAC a cikin wata sanarwa da ya fitar ta ce, ta amince da jimillar kudi naira biliyan 903.480 daga kudaden shigar da ake da su domin rabawa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp