Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Nijeriya (FAAN) ta umarci dukkanin kamfanonin jirgen sama da su kwashe jiragensu daga babban filin sauka da tashin jiragen kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja zuwa wasu filayen jiragen saman na daban.
FAAN, a wata sanarwar da ta fitar a ranar 8 ga watan Mayu da aka fitar a ranar Talata ga kamfanonin, na cewa, a ranar 29 ga watan Mayu ne za a kaddamar da bikin rantsar da sabon shugaban kasar Nijeriya, don haka ne dukkanin matakan da za a bi wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali to dole a dauka.
- Wani Babban Dalilin Da Ya Haifar Da Hargitsi A Kasar Sudan
- An Kammala Gasar “Gadar Sinanci” Ta Daliban Jamio’in Masar
“Don haka, ake bukatar ku kwashe jiragenku (a matakin wucin gadi) zuwa wasu filayen jiragen daban sakamakon bikin amsar mulki na sabon shugaban kasa da zai gudana a ranar 29 ga watan Mayun 2023.”
Sanarwar mai lambar alama: FAAN/ABJ/NAIA /RGM/NC/AM/1000/VOl-1 dauke da sanya hannun manajan shiyya da ke kula da yankin arewa ta tsakiya, Kabir Mohammed, ya ce, “Bikin rantsar da shugaban kasa wani babban lamari ne da ya shafi batun tsaro sosai, domin tabbatar da kiyaye lafiya da tsaro ga kowani bangare, akwai bukatar a matakin wucin gadi ku kwashe dukkanin jiragenku da ke GAT zuwa wasu filayen jiragen na daban.
“Kan hakan, ana rokonku da ku sauya ma jiragenku matsugini gabanin ko kafin ranar 22 ga watan Mayun 2023.”
FAAN ta nemi jiragen da su ba da hadin kai domin tabbatar da komai ya tafi cikin tsari da ingancin tsaro.