Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ta sanar da cewa gobe Alhamis ce daya ga watan Zul Hajji.
Sanarwar da ta fito daga Sarkin Malaman Sakkwato, Malam Yahaya Muhammad Boyi ta tabbatar da cewa, Alhamis 30 ga watan Yunin 2022 ita ce ta zama ranar ɗaya ga watan Zul Hajji ta shekarar Hijira ta 1443.
Wakilinmu ya samu sanarwar ce ta hanyar sakon waya daga Sarkin Malaman.
Dama dai fadar ta Sarkin Musulmi ta sanar da ‘Yan Nijeriya su fara duba tsayuwar sabon jinjirin wata na Zul Hajji wanda yake zama wata na 12 a cikin kalandar shekarar Musulunci ta Hijira.