Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin da ke cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kwatanta matakan da tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka ɗauka dangane da cire ko dakatar da gwamna a lokacin da suke kan mulkinsu ba. Ta ce irin waɗannan rahotanni ba gaskiya ba ne, kuma an kirkire su ne saboda a tayar da ƙurar siyasa.
A wata sanarwa da Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Jumma’a, an bayyana zargin a matsayin ƙarya mai cike da soki-burutsu, tare da musanta jita-jitar cewa Shettima ya soki Shugaba Tinubu dangane da rikicin siyasa da ya faru a Jihar Ribas.
- Wanda Ya Yi Gangancin Taba Takarar Shettima Ya Gayyato Wa APC Faɗuwa A 2027 – Aminu Boyi
- Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima
Sanarwar ta bayyana cewa jawaban da Mataimakin Shugaban Ƙasa ya yi a wajen ƙaddamar da littafin “OPL 245: The Inside Story of the $1.3 Billion Oil Block” wanda tsohon Antoni Janar na Tarayya, Mohammed Bello Adoke (SAN), ya rubuta, sun waiwaye ne kan tarihin baya saboda muhimmancin adana tarihin gwamnatoci, amma ba shi da alaƙa da sukar Shugaba Tinubu.
“Wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da mutane sun juyar da kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasa don cimma wata mummunar manufa,” cewar sanarwar. “Sun juya bayanin yadda gwamnatin Jonathan ta taɓa tunanin tsige Shettima daga matsayin gwamna a lokacin da rikicin Boko Haram ya yi tsanani.”
Sanarwar ta jaddada cewa Shettima yana bayar da labarin abubuwan da suka faru fiye da shekara goma da suka gabata, kuma ya yi haka don jinjina wa kyakkyawan halin Adoke a matsayin ma’aikacin gwamnati.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yunƙurin da aka yi na haɗa waɗannan maganganun da abubuwan da suka faru a Jihar Ribas, musamman batun dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ayyana dokar ta-baci, fassara ce da aka yi ta ba daidai ba, ko kuma suka ne ga kundin tsarin mulkin ƙasa.
“Domin kaucewa ruɗani, Shugaba Tinubu bai cire Gwamna Fubara daga mukaminsa ba,” sanarwar ta jaddada. “Abin da aka aiwatar dokar dakatarwa ce, ba tsige wa ba. Wannan mataki da kuma ayyana dokar ta-baci an ɗauke su ne sakamakon rikicin siyasa mai tsanani da ya faru a Jihar Ribas a wancan lokacin.”
Sanarwar ta ce rikicin da ya faru a Ribas ya cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya gindaya na ɗaukar matakan gaggawa, bisa tanadin Sashe na 305(3)(c), wanda ke bayar da damar hakan idan an samu rashin zaman lafiya da tsaro a matsayin matakin da ya zama wajibi a yi amfani da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp