Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton da ke cewa an hana Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shiga fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya ce labarin ƙarya ne kuma yana da nufin kawo ruɗani.
- Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)
- Dantsoho Ya Bukaci ‘Yan Kasuwa Su Yi Amafani Da Damar Fitar Da Kaya Zuwa Ketare
Ya ce babu wani shinge na soja ko wani da ya hana Shettima shiga fadar, kuma wannan zance ba gaskiya ba ne.
Ya kuma ƙaryata jita-jitar tallan takarar shugabanc ƙasa ta shekarar 2027 da ke ɗauke da hotunan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, yana cewa wani yunƙuri ne na tayar da hankali.
Nkwocha ya ce dangantaka tsakanin Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa tana nan daram, kuma Shettima yana mayar da hankali ne wajen goyon bayan manufofin gwamnati.
Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da irin waɗannan labaran ƙarya, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatar da gaskiya labari kafin wallafawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp