Mai bai wa shugaban kasa shawara ta fannin bunkasa zamantakewa, Miss Maryam Uwais ta bayyana cewa sakamakon karuwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya ya sa gwamnatin tarayya ta bullo da shirin tsamo yara daga hatsari (ARC-P).
Wannan shiri ne da zai magance matsalar da yara da kuma matasa suke fuskanta a dukkanin jihohin kasar nan ciki har da Babban Birnin Tarayya.
- Mahara Sun Kashe ‘Yansanda 3 A Wani Hari Da Suka Kai Enugu
- Peng Liyuan Ta Ziyarci Kwalejin Nazarin Kide-Kide Na Princess Galyani Vadana
Da take jawabi a wurin taron kara wa juna sani na kwanaki uku da za a horar da matasa har sama da 900 a Maiduguri da ke Jihar Borno, Misis Maryam wacce ta kasance jagorar shirin karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa, ta bayyana cewa an samar da wannan shirin ne domin magance matsalolin da ke addabar yara da kuma matasa a fadin Nijeriya, wajen yin amfani da wasu matakai da suke da alaka da ilimi da lafiya da horar da sana’o’in da noma da kuwa wasanni.
Misis Maryam wadda ta samu wakilcin mataimakin daraktar kasafi da tsare-tsare, Grace Akpabio ta ce za a gudanar da bayar da horon ga matasa a Jihar Borno har na tsawan makonni uku, domin samar musu da sana’o’in dogaro da kai.
A cewar mashawarciyar shugaban kasan, horar zai bunkasa basirar matasan wanda zai yi daidai da shirin ARC-P wajen tallafa wa rayuwarsu da kuma al’umma. Ta kara da cewa matasan da za su amfana da shirin suna da matukar rawar da za su taka wajen cimma nasarar wannan shirin wanda gwamnatin tarayya ta kaddamar tare da tallafin bangaren ‘yan kasuwa masu zaman kansu.
A nasa jawarin, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya yaba wa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC na samar da shirin ARC-P. Ya ce a yanzu haka shirin yana gudana a kasa wanda zai shafe shekaru 25 yana gudana.
Zulum wanda ya samu wakilcin kwamishinan harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo ya ce gwamnatin tarayya ta samar da shirye-shirye kamar irinsu ARC-P wadanda za su taimaka wajen magance matsalolin yara da matasa da mata musamman a yankin arewa maso yamma da yakin Boko Haram ya daidaita a tsawan shekari 12 da suka gabata.
Gwamna Zulum ya sha alwashin hada kai da tawagar shirin ARC-P wajen bayar da goyon baya domin shirin ya samu nasara, yayin da kuma ya yi kira ga matasan su jajirce wajen ganin sun amfanar da rayuwarsu kan wannan shirin.