Fadar shugaban kasa, ta musanta dawo da ci gaba da biyan tallafin man fetur, inda ta jaddada kudirinta na janye tallafin don alfanun kasa baki daya.
Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewar gwamnatin tarayya, ta yi hasashen kashe Naira tiriliyan 5.4 2024 wajen biyan tallafin man fetur.
- Kotu Ta Bayar Da Umarnin Aike Wa Ganduje Da Wasu Sammaci Ta Wasu Hanyoyi Daban
- Samun Bunkasuwa Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
Amma, cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan bayanai, Bayo Onanuga, ya bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin.
Ya ce, “An jawo hankalin fadar shugaban kasa kan takardun manufofin kasafin kudi guda biyu wanda kafafen yada labarai ke yadawa.
“Muna kira ga jama’a da kafafen yada labarai da su yi watsi da wadannan takardu guda biyu su daina tattaunawa a kansu. Babu wani daftari da gwamnati ta amince da shi.”
Ya gargadi kafafen watsa labarai da suke bin diddigin bayanai yadda suke da kaucewa yada abin da zai haifar da rudani.