An alkanta raguwar darajar Naira a watannin baya, a matsayin babbar koma bayan da ya sanya aka samu ruguwar shigo da kaya daga ketare, zuwa cikin kasar nan.
Wasu kwararrun masu fashin baki a fannin tattalin azrkin kasa a FBNKuest sun alakanta jinkirin da aka samu na shigo da kaya daga waje, kan abubawa da dama.
- Kasar Sin Ta Karrama ’Yan Sama Jannati 3 Na Kasar Da Lambobin Yabo
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
Wadannan abubuwan sun hada da; faduwar darajar Naira, a watan Disambar 2024, raguwar shigo da kayan abinci na tallafi, saboda tsadar kudaden musaya da kuma gabatar da batun bayar da damar shigo da kayan abinci a cikin kawanuka 150, da Gwamnatin Tarayya, ta shelanta, a 2024.
Hauhawan shigo da kaya ya samar da saukin zuwa kashi 41.29 a watan Disambar 2024, wanda hakan ya sanya ya kai na raguwar da aka samu a karo na farko, a watan Satumbar 2019.
Shugaban Cibiyar hada-hadar kasuwanci mai zaman kanta ta CPPE Muda Yusuf, ya alakanta hakan kan zamanantar da kudaden musaya na sauye-auyen da aka samar da kuma daukin ba Babban Bankin Nijeriya CBN, ya samar kan kudaden musaya.
A cewar Yusuf, hasashe kan kudaden na musaya ya dora kara samar da daidaito a 2025.
Wannan sa ran da ake yi, abubuawa da dama ne, suka haifar d hakan wadanda suka hada da; karin da aka samu a kudaden ajiya na kasar waje, wadanda suka kai yawan dala biliyan 40.
Kazalika, an kuma samu kari a kan kudaden da ake turawa na kasa da kasa MTOs da kuma kudaden da aka tura daga ketare.
Bugu da kari, kara karfafa tafiyar da kudaden musaya da Babban Bankin Nijeriya CBN, kan daukin da bankin ya samar, ya kara janyo hakan.
Rarar kudaden ketare na kasar nan na dala biliyan biyu da kuma samun nasara kan bayar da dala miliyan 500 ya kara haifar da hakan.
Matsayar da aka cimma kan bin ka’dojin dala biliyan kudaden musaya da Babban Bankin Nijeria CBN ya yi, hakan ya sanya an kara samun wani sauki.
Ana kuma sa ran radadin rage shigo Man Fetur da Matatar Mai ta Dangote ta yi, ta hanyar kafa matatar a kasar nan da kuma sa ran da ake yi na idan an kammala aikin matatun Mai na garin Warri da ta Fatakwal, hakan zai samar da sauki kan kudaden musaya, wanda kuma hakan, zai kara samar da damar shigar kudaden musaya, zuwa cikin kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp