A shekarar nan ta 2024, tattalin arzikin duniya na ci gaba da samun raguwar bunkasa, kuma ana ta fama da rashin tabbas a yanayin siyasar duniya, inda musamman wasu kasashe ke kara ba da kariya ga harkokin kasuwanci, lamarin da ya yi tasiri ga harkokin ciniki, da karuwar zuba jari a duniya. A cikin irin wannan yanayi, an gudanar da babban taron ayyukan tattalin arziki na koli na shekara-shekara a birnin Beijing na kasar Sin, daga ran 11 zuwa 12 ga watan nan, wanda ya kawo kwanciyar hankali da tabbas.
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yi imanin cewa, a shekarar 2025, kasar Sin za ta kara himmantuwa wajen tinkarar kalubalen tattalin arziki da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikinta, wanda hakan zai yi tasiri sosai ga tattalin arzikin kasar Sin, har ma da kasuwannin duniya baki daya.
- Shugaba Xi Jinping Zai Halarci Bikin Cikar Yankin Macao Shekaru 25 Da Komowa Kasar Sin
- Nazari Kan Cututtuka 8 Da Ke Kama Zomo Da Hanyoyin Mangance Su
Taron ya ce, ana dab da cimma manyan burika da kammala ayyukan raya tattalin arziki da zamantakewa cikin nasara a cikin shekarar nan ta 2024, kuma hakan ba abu mai sauki ba ne. Duba da cewa, a cikin watanni 9 na farkon shekarar bana, yawan karuwar GDPn kasar Sin ya kai sahun gaba a tsakanin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya. Kana a cikin watanni goma na farkon bana, jimillar yawan cinikin shige da ficen kayayyaki na kasar Sin ya kai wani sabon matsayi a tarihi a tsakanin wannan lokaci. Kaza lika, ci gaban sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko na kasar Sin na kan gaba a duniya…Wadannan nasarorin da aka cimma na zahiri, sun tabbatar da cewa, yanayin da ake ciki na ci gaban tattalin arzikin kasar Sin cikin dogon lokaci bai canza ba, kuma har yanzu kasar Sin ta kasance “inji mafi muhimmanci” na ci gaban tattalin arzikin duniya.
“Bude kofa” tabbataccen halin musamman ne na tattalin arzikin kasar Sin. Kana ya sa babban darekta, kuma babban jami’in zartaswa na kamfanin Zeiss na kasar Jamus reshen kasar Sin Maximilian Foerst, ya yi hasashen cewa, kasar Sin za ta zama babbar mai samar da arziki a duniya. A cewarsa, “Kasuwar kasar Sin tana da girma, wadda ba za mu iya yin watsi da ita ba.”
Baya ga yadda take kara kokarin tabbatar da ci gabanta, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kudurin fadada bude kofarta ga kasashen waje, kuma burinta na maraba da masana’antu daga dukkan kasashen duniya, don raba damar samun ci gaba yana nan daram. (Mai fassara: Bilkisu Xin)