Ma’anar Tawakkali:
Babban malami Muhammad ɗan Ahmad Ibnu Juzai a-Kalbi Allah Ya ji ƙan sa yana cewa:
التَّوَكُّلُ هُوَ الِاعْتِمَادُ عَلَى اللهِ فِي تَحْصِيلِ الْمَنَافِعِ أَوْ حِفْظِهَا بَعْدَ حُصُولِهَا، وَفِي دَفْعِ الْمَضَرَّاتِ وَرَفْعِهَا بَعْدَ وُقُوعِهَا.
Fassara:
“Tawakkali yana nufin dogaro ga Allah wajen samun alherai ko kiyaye su bayan an same su, da kuma dogaro da Shi wajen kawar da masifu da kuma ɗauke su bayan sun faru.” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [1/122].
Fashin Baƙi:
Maganar da Ibn Juzai ya fadi a kan tawakkali tana bayyana ainihin ma’anar dogaro ga Allah cikin dukkan al’amura na rayuwa, wato samun alheri, da kiyaye shi, da kuma kauce wa masifa, ko kuma fita daga cikin masifa idan ta afku. Tawakkali yana nufin dogaro ga Allah da zuciya ɗaya tare da yin ƙoƙari da dalilan da Allah ya tanadar don cimma buri. Ba wai kawai mutum ya jingina da Allah ba tare da yin aiki ba, ko kuma ya dogara da aikinsa ba tare da tawakkali ba, sai dai a haɗa su duka.
Bangarorin Tawakkali:
Ibnu Juzai ya kasa tawakkali zuwa manyan bangarori guda biyu:
● Tawakkali wajen samun alheri ko kiyaye shi. Mutum ya riƙa dogara da Allah wajen samun ni’ima kamar arziki, da lafiya, da ilimi, da duk wani alheri.Idan mutum ya sami alheri, to yana buƙatar tawakkali don kiyaye shi, saboda shi kansa alheri yana buƙatar kulawa da albarka daga Allah.
● Tawakkali wajen kawar da masifa ko saukinta bayan ta afku. Idan mutum yana fuskantar wata musiba kamar talauci, ko rashin lafiya, ko wata matsala, zai dogara ga Allah don samun sauki. Idan masifa ta riga ta faru, mutum yana tawakkali wajen samun mafita da sauƙin abin da ya same shi a wurin Allah.
A Musulunci, tawakkali ba yana nufin mutum ya zauna ba tare da yin aiki ba. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Da kun yi tawakkali ga Allah da gaske, da ya ciyar da ku kamar yadda yake ciyar da tsuntsaye. Suna fita da sassafe cikinsu da yunwa, kuma suna dawowa da yamma cikinsu a ƙoshe.” Hadisi ne ingantacce Tirmizi da Ɗabarãni ne suka ruwaito.
Wannan hadisi yana nuna cewa tsuntsaye ba sa zama kawai suna jiran Allah ya ciyar da su, sai dai suna aiki ta hanyar sammako neman abincinsu a wurin Allah. Haka ma mutum yana tawakkali ga Allah amma yana yin kokari da aiki tuƙuro da dogaro ga Allah domin kaiwa ga gaci.
Tawakkali yana daga cikin manyan siffofin muminai kamar yadda Allah Ya ce a cikin Alkur’ani: “Kuma ga Allah kaɗai za ku dogara, idan kun kasance ku mummunai ne” Suratul Mã’idati aya ta 23.
Fa’idojin Tawakkali:
Fa’idodin tawakkali sun haɗa da:
• Samun kwanciyar hankali da nutsuwa.
• Rage damuwa da fargaba.
• Samun kariya daga Allah.
• Samun albarka da nasara a rayuwa.
Bambancin Tawakkali da Riƙon Hannu (Tawãkul):
Akwai bambanci tsakanin tawakkali da tawaakul: Domin tawakkali yana nufin dogaro ga Allah tare da yin aiki. Shi kuma tawãkul k yana nufin nuna jingina ga Allah ba tare da bin tsarin da Allah Ya shimfiɗa na riskar abubuwa ba.
A taƙaice, Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, yana nuni da cewa tawakkali yana rufe dukkan fannoni na rayuwar mutum wajen neman alheri da kiyaye shi, har zuwa kauce wa masifa da fita daga gare ta. Tawakkali yana buƙatar cikakken imani da Allah tare da bin hanyoyin da suka dace da Allah Ya tsara na samun abubuwan rayuwa. Wannan shi ne ainihin fahimtar tawakkali a Musulunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp