Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi rangadi a wurare daban daban kafin bikin bazara na kasar, kana kafin bikin na wannan shekara, shugaban ya ziyarci lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin. Sai dai wadanne fannonin ya mai da hankali a kai, yayin wannan ziyara?
Abu na farko da shugaba Xi ya lura da shi, shi ne aikin sabunta fasahohin masana’antu. A rangadinsa na wannan karo, shugaban ya ziyarci wata masana’antar sarrafa kayayyakin karfe, inda ya duba yadda ake kokarin amfani da sabbin fasahohi a wurin, kana ya nanata bukatar samar da kayayyaki masu inganci, wadanda ba za su gurbata muhalli ba.
- Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari
- Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru Kan Naira Biliyan 64
Sa’an nan abu na biyu da shugaba Xi Jinping ya sa lura a kai shi ne yadda ake kula da jama’ar da bala’in ambaliyar ruwa ya ritsa da su a bara. Yayin da fanni na uku shi ne yadda kasuwannin wurin suke samar da isasshen kayayyakin abinci masu inganci ga jama’a, a lokacin bikin bazara na gargajiya.
Cikin wata unguwa, shugaba Xi ya ce, wani abu mafi faranta rai shi ne ganin yadda jama’a suke jin dadin rayuwa. Ya ce ya kamata a kara kokarin tabbatar da haka a ko da yaushe. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp