Allah ya taimake ni da na yi kacibis da wani rubutu mai taken: “Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma” wanda wani bakon marubuci, Mukhtar Anwar, ya wallafa a Jaridar Leadership Hausa ta ranakun 10/10/25, 17/10/25 da 24/10/25.
A fahimtata Mukhtar Anwar, ba wai bakon marubuci ba ne kawai, sabon marubuci ne; wanda yake rubutu a kan wani abu ba tare da ya yi bincike ya san gaskiyar al’amarin ba, watakila don neman suna ko biyan wata bukatarsa ta son zuciya.
- Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
- Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule
A rubutun nasa, ya yi kokarin kwatanta yadda ‘yan fansho suka ji dadi ko suka wahala a zamanin Gwamnatocin Mallam Ibrahim Shekaru, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Har ila yau, ya bayyana cewa; lokutan Mallam Ibrahim Shekarau da Alhaji Abba Kabir Yusuf, ‘yan fansho sun ji dadi kawarai da gaske, yayin kuma da suka sha wahalaha matuka gaya a lokutan Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Anwar ya ce, “Tsohon Gwamna Kwankwaso da Tsohon Gwamna Ganduje, ba su zamto masu tausayi da jin kan ma’aikatan gwamnati ba a Kano, musamman wadanda suka ajiye aiki.” Ya kara da cewa, Kwankwaso da Ganduje; sun yi tarayya “wajen haifar da da maras ido ga rayuwar tsoffin ma’aikata a Kano, sabanin lokacin mulkin Shekarau ko gwamna mai ci, Abba Gida-Gida.”
Haka zalika, ya kafa hujjojinsa a kan “Rashin biyan ‘yan fansho a kan lokaci”, “Jigata’Yan-fansho Da Sunan Tantancewa”, “Jefa Razani A Zukatan Maikata”, da ”Salwantar Da Kudaden ‘Yan-fanshon”.
Wadannan bayanai na Anwar, sun tabbatar da ko dai bai san abin da ya faru a Hukumar Fansho a lokutan da Kwankwaso ya yi Gwamnan Kano ba, ko kuma shi dan kanzagin wani dan siyasa ne da yake so ya kambama, duk da tauraruwarsa ta disashe. Duk wanda ya san yadda mulkin Kwankwaso ya inganta rayuwar ‘yan fansho a Jihar Kano, ya san cewa; duk abubuwan da Anwar ya fada ba gaskiya ba ne.
A tarihin biyan fansho da garatuti a Jihar Kano, babu lokacin da ‘yan fansho suka ji dadi; irin lokutan mulkin Kwankwaso na farko da na biyu, sabanin abubuwan da Mukhtar Anwar ya rubuta bisa dalilai kamar haka:
1- Lokacin da Kwankwaso ya karbi mulki a hannun soja a 1999, ya gaji basussuka masu yawan gaske na kudin sallamar ma’aikata da suka bar aiki, wato garatuti. Wannan ya sa ya rika bai wa Hukumar Fansho Naira miliyan ashirin duk wata, har sai da aka tabbatar an gama biyan duk wani mai hakki hankkinsa. A wancan lokacin, Hukumar Fansho har sanarwa ta rika bayarwa a gidajen rediyo da talibijin cewa; duk dan fanshon da bai karbi hakkinsa ba, ya zo ya karba. Kadan daga cikin wadanda wannan sanarwa ta amfana, sun hada da wasu masu hakan rijiya, wato Ganga, da suka bar aiki shekara da shekaru suka zo daga Sumaila suka karbi hakkinsu, suna godiya da farin ciki.
Kazalika, a lokacin ne; gwamnatin Kwnkwaso ta kashe jinginar da katin biyan fansho da ‘yan fansho ke yi idan sun shiga mawuyacin hali na rashin kudi. An yi haka ne, ta hanyar kama masu jinginar da katin fansho da gurfanar da su gaban shari’a, inda aka hukunta su tare kuma da bude wani asusu da Hukumar Fansho ta yi ta sa kudi da aka rika bai wa ‘yan fanshon rance, idan bukata ta kama su kafin a biya su fanshonsu a karshen wata.
2- Haka kuma, a lokacin mulkin Kwankwaso na biyu, 2011 zuwa 2015, kowa ya san ‘yan fansho sun ji dadi fiye da kowane lokaci a Jihar Kano sakamako:
·Biyan ‘yan fansho hakkinsu a kan-kari: Ma’aikata da dama sun karbi kudin sallamarsu (Garatuti), kafin sanarwar da suka bayar ‘notis’, ta wata uku ta kare. Kazalika, wannan ya bayar da damar saka su cikin jerin masu amsar fansho a watan da wa’adin nasu ya kare. Na tabbatar da masu ruwa da tsaki a kan harkar fansho na Jihar Kano a wannan zamani da suka hada da ‘yan fansho, da ma’aikatan Hukumar Fansho da sauran shugabannin ‘yan fansho shaida ne.
·Karin kudin fansho: Lokacin da Kwankwaso ya dawo mulki karo na biyu, akwai ‘yan fanshon da fanshonsu Naira 350 ne kacal. Tausayawa kananan ‘yan fansho ya sa Kwankwaso ya kara kudi, ta yadda mafi karancin fansho ya koma Naira 5,000, sannan kuma kowane dan fansho, sai da aka kara masa kudi gwargwadon fanshonsa.
Haka zalika, Abba Kabir Yusuf ya kara kudin fansho zuwa mafi karanci na Naira 20,000. Kwankwaso da Abba ne kadai na san sun taba kara wa ‘yan fansho kudi a Jihar Kano.
·Tantance ‘yan fansho jefi-jefi ya zama wajibi, saboda a cire sunayen wadanda suka rasu daga jerin sunayen ‘yan fansho, tunda ba koda-yaushe ake sanar da hukuma idan dan fansho ya mutu ba.
A lokacin Kwankwaso, ba a tilasta wa tsoho tukuf da marar lafiya da wanda yake nesa zuwa tantancewa. A kan tashi ma’aikata ne su je har gidan wanda abin ya shafa a ko’ina yake a Nijeriya, a tantance shi; don ci gaba da biyansa hakkinsa. Wannan hanya ce ta saukaka wa ‘yan fansho, ba jigata su kamar yadda Anwar ya ce an yi ba, wai har wadansu suka rasa rayukansu a layin tantancewa. Wal iyazu billah!
·A wannan lokaci, Hukumar Fansho ta kafa kwamitin tallafa wa ‘yan fansho, karkashin babban sakatare mai ritaya, aka zuba Naira miliyan goma, domin tallafa wa ‘yan fansho ta hanyar ba su rance, ko sayar musu da kayan masarufi cikin sauki da arha; don saukaka wa rayuwarsu.
·Zargin biliyoyin kudaden ‘yan fansho sun salwanta a hannun Kwankwaso ba gaskiya ba ne. Kudaden da mara-sa-kan-gado ke zargin sun bata, an yi amfani da su ne wajen gina unguwannin Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo a Kano bisa ka’ida, sannan kuma duk hukumomin binciken Nijeriya, sun bincika sun tabbatar da hakan gaskiya ne. Wannan shi yasa kowa ya zauna lafiya, ba tare da tsangwama ba.
Ina fata wannan dan bayani da na yi, ya tabbatar wa da Mukhtar Anwar da sauran jama’a baki-daya cewa; a lokutan da Kwankwaso ya yi mulki a Jihar Kano, ana biyan ‘yan fansho hakkokinsu a kan lokaci, ba tare da jefa su cikin razanin za a biya su ko ba za a biya su a kan kari ba, bayan sun yi ritaya.
Bugu da kari, ba a jigata ‘yan fansho wajen tantancewa, har su galabaita ko su rasa rayukansu a layin tantancewa ba; sannan kuma Kwankwaso bai salwantar da kudaden ‘yan fansho ba, hasali ma tanadi ya yi musu ta hanyar gina gidaje, domin amfanin gaba.
A karshe, duk abubuwan da Mukhtar Anwar ya fada a kan maigirma Kwankwaso da gwamnatinsa, a kan biyan ‘yan fansho hakkokinsu lokutan da ya yi mulkin Kano, ba gaskiya ne ba, kuma ya zalunce shi da kuma mu da muka taimaka masa wajen sauke nauyin shugabanci. Amma wata shari’ar, sai a lahira.













