• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Faransa Ta Aike Da Sojojinta Kasashen ECOWAS Don Shirin Kai Wa Nijar Hari

by Muhammad
2 years ago
Faransa

TRT ta rawaito cewa, Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a watan Yuli sun yi zargin cewa Faransa tana tura sojojinta zuwa kasashen Yammacin Afirka da dama da zummar yin amfani da “kafin soji” a kansu.

“Faransa tana ci gaba da kai dakarunta kasashen kungiyar ECOWAS da dama a wani bangare na shirin kaddamar da hare-hare kan Nijar, wanda take kitsawa tare da hadin gwiwar kungiyar,” a cewar kakakin sojojin Kanar Amadou Abdramane a wata sanarwar da ya karanta a gidan talabijin na kasar ranar Asabar da maraice.

  • Har Yanzu Jakadan Faransa Bai Fice Daga Jamhuriyar Nijar Ba – Macron
  • Juyin Mulki: Aljeriya Ta Bukaci Sojin Nijar Su Mika Mulki Cikin Watanni 6 Kacal

Ya ce Faransa ta tura dakarunta kasashen da suka hada da Senegal, Benin da Ivory Coast, a wani bangare na ”shirin kaddamar da hari” a kan Nijar.

Kawo yanzu dai Faransa ba ta yi martani kan wanna zargi ba.

Amma Kanar Abdramane ya yi ikirarin cewa ranar 1 ga watan Satumba Faransa ta tura jiragen soji biyu da kuma wani jirgi samfurin Dornier 328 domin karfafa dakarunta da ke Ivory Coast, yayin da kuma ta tura jiragen helikwafta biyu samfurin PUMA da motoci masu silke 40 zuwa Benin.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Ya kara da cewa ranar 7 ga watan Satumba wani jirgin ruwan yakin Faransa ya isa Cotonou babban birnin Benin dauke da dakaru.

Ranar Litinin Firaiministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce sojojin suna tattaunawa da Faransa da zummar tabbatar da “gaggawar” kwashe dakarunta daga kasar.

Sai dai sojojin sun zargi Faransa da “rashin gaskiya da jan-kafa da kuma kafar-ungulu” don kawai ta kawar da su.

Dangantaka tsakanin Faransa da Nijar ta yi tsami bayan Paris ta dage cewa dole sojoji su mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kan mulki bayan juyin mukin da suka yi masa ranar 26 ga watan Yuli.

Juyin mulkin ya sa kungiyar ECOWAS ta kakaba wa Nijar takunkumai sannan ta yi barazanar amfani da karfin soji idan aka gaza cimma matsayar mayar da Bazoum kan mulki ta hanyar diflomasiyya.

Faransa tana da dakaru sama da 1,500 a Nijar wadanda suke hadin-gwiwa wajen yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel, sai dai sojojin kasar sun soke dangantakar da ke tsakaninsu da kasar tun bayan juyin mulki.

Hasalima sun umarci jakadan Faransa ya fita daga Jamhuriyar Nijar, ko da yake har yanzu yana kasar.

Dubban mutane ne suka rika gudanar da zanga-zangar kin jinin Faransa a Yamai, inda suka bukaci kasar ta kwashe dakarunta daga Nijar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai
Labarai

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

October 30, 2025
Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 
Manyan Labarai

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
Manyan Labarai

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025
Next Post
AU Ta Zama Mamba Ta Dindindin A Kasashen G20 Masu Karfin Tattalin Arziki A Duniya

AU Ta Zama Mamba Ta Dindindin A Kasashen G20 Masu Karfin Tattalin Arziki A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray

October 30, 2025
Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya

October 30, 2025
Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

October 30, 2025
Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba

October 30, 2025
Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

October 30, 2025
Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

October 30, 2025
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15

October 30, 2025
Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.