Rahoton AFEX, ya ce, ya yi hasashen samun hauhawar farashin masara da shinkafa a shekarar da muke ciki ta 2024.
Rahoton wanda aka fitar ranar Laraba a Legas, ya yi hasashen samun hauhawar farashin masara da kashi 25% da kuma karin kashi 40 cikin 100 na farashin shinkafa.
A shekarar 2023, an samu sauyi mai yawa a farashin masara, inda ya kai N550,000 a cikin farko-farkon shekara, sai farashin ya rufe shekarar da kan farashin kudi N480,000. Rahoton ya danganta karuwar da raguwar kayan kan tasirin rikicin Rasha da Ukraine a farashin taki.
A bangare guda ana hasashen farashin makamashi zai ragu da kashi 5 cikin 100 a shekarar 2024 sannan ya kara raguwa da kashi 0.7 a shekarar 2025. Ana sa ran kayayyakin noma za su samu raguwar kashi 2 cikin 100 a shekarar 2024 da raguwar kashi 3 a shekarar 2025, wanda ake alakanta hakan kan rikicin Gabas ta Tsakiya.
Oluwafunto Olasemo, Mataimakin Shugaban Kasuwannin Kudi a AFEX, ya jaddada mahimmancin hangen nesa wajen daidaita hanyoyin kasuwanci da motsi a tsakanin ‘yan wasan kasuwa na zahiri da na sakandare.
Ya lura da rikitattun abubuwan daidaita yanayin siyasa, tattalin arziki, da muhalli a cikin kasuwar kayayyaki.
Olasemo ya jaddada bukatar bunkasa noma a cikin gida, daidaita kasuwanci da samar da tsare-tsare don dakile wannan matsalar da tabbatar da samar da wadataccen abinci.
Rahoton ya kuma ba da shawarar a amince da tsarin noma mai ɗorewa kamar jujjuyawar amfanin gona don inganta ƙarfin ƙasa da haɓaka yawan aiki, wanda zai iya ƙara samar da kuɗin noma da kashi 21%.
A shekarar da ta gabata alakanta samuwar irin wadannan matsaloli da kan girgizar kasa da karancin makamashi da tashe-tashen hankula da suke da jibi da siyasa da karancin kudi. Duk da waɗannan ƙalubalen, kasuwar kayayyaki ta duniya ta ragu da 24% a cikin 2022.
Kasuwanni a Nijeriya sun fuskanci koma baya sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da sauye-sauyen tattalin arziki, wanda ya haifar da karuwar kashi 0.63% a kashi uku na farkon shekarar 2023.
An samun hauhawar farashin kayayyakin noma a Nijeriya a farko saboda karancin wadata da kuma karuwar bukatar kasashen duniya.