Farashin tikitin jiragen sama a Nijeriya ya yi tashin gwauron-zabi yayin da kamfanonin zirga-zirga ke fama da tsadar man jirgi da kuma faɗuwar darajar naira.
Wani labari da kafar yada labaraibta BBC ta wallafa a shafinta, ya bayyana cewa, a ranar Juma’a sun nuna cewa farashin tikitin jirgi na Azman Air daga Legas zuwa Kano da Kaduna ya tashi daga kamar N60,000 zuwa N100,000.
- Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Jigila Kai Tsaye Zuwa Sin Da Indiya
- Yajin Aikin ASUU: Dalibai Sun Yi Barazanar Rufe Tituna, Tashoshin Jirgin Sama Da Na Kasa
Shi ma kamfanin Max Air ya ƙara farashin zuwa Kano daga Abuja zuwa N79,000 mafi ƙaranci.
Shi ma kamfanin Air Peace ya ce farashin tikitinsa daga Legas zuwa Abuja ya koma N80,000, komawa kuma N85,000.
Ibom Air ma ya mayar da farashin zuwa N80,000 daga Legas zuwa Abuja, yayin da za a biya N130,000 a Max Air kan tikitin Fatakwal zuwa Kano.
Yayin wata ganawa da suka yi da Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika a ranar Talata, ƙungiyar masu zirga-zirgar jiragen ta koka kan farashin man jirgin na jet A1 da suka ce ya kai kusan N100 kan kowace lita ɗaya.
Duka wannan na faruwa ne baya ga tsaiko na tsawon awanni da fasinjoji ke fuskanta a filin jirgi kafin tashinsa a mafi yawan lokaci.