Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle ya bayyana cewa, sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi na inganta manufofin tattalin arziki sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro, Mista Henshaw Ogubike, ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
- NEMA Ta Bayar Da Tallafin Kayan Agaji Ga Wadanda Harin ‘Yan Bindiga Ya Shafa A Zamfara
- Shirin NG-CARES: Gwamna Lawal Ya Tallafawa Mutane 44,000 Da Fiye Da Naira Biliyan 4
Matawalle ya ce, wadannan tsare-tsare da suka hada da sabbin sauye-sauyen haraji da kuma nasarori da dama da aka samu a bangarori daban-daban sun ba da gudummawa wajen kawo sauyi a tattalin arzikin kasar nan.
Ya kara da cewa, wannan sauyin da aka samu a fannin tattalin arziki zai amfanar da dukkan ‘yan Nijeriya nan gaba.
Don haka, ya bukaci masu sukar gwamnatin Tinubu, musamman daga sassan Arewacin Nijeriya da su kasance masu kyakkyawar fata.