Sojoji sun harbe ‘yan bindiga uku a wani artabu bayan sun kwato wasu shanun da suka sace a kauyen Kurutu da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
Wani shugaban al’ummar yankin wanda ya tabbatar wa Daily Trust da labarin ta wayar tarho a ranar Talata, ya ce an kwato shanu da tumakin ne a ranar Asabar a dajin Hayin-Dam, wanda a cewarsa yana iyaka da al’ummar Janjala a karamar hukumar Kagarko.
- Farfaɗo Da Tattalin Arziƙi: Sauye-sauyen Tinubu Ya Fara Haifar Da Sakamako Mai Kyau – Minista
- Cinikin Shige Da Ficen Kasar Sin Na Samun Bunkasuwa Mai Dorewa
Ya ce, ‘yan bindigar sun kai farmaki ne wata rigar Fulani a kauyen Kurutu inda suka yi awon gaba da wasu shanu tare da raunata wasu makiyaya biyu.
Ya ce sojojin sun kai makiyayan biyu da suka jikkata zuwa asibiti a kauyen Katari da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
- Ba a samu damar jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Hassan Mansur ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.