Yana daga cikin wadannan maganganun nasa masu nuna fasaha da balagar harshensa (SAW), abin da ba zai yiwu a yi kamanceceniya da su ba (a ce da maganar Annabi da ta wane iri daya ce) kuma ba a fito-na-fito wajen Balaga. Kamar fadinsa mai tsira da aminci cewa “Almuslimuna tatakafa’u dima’uhum – Musulmai jininsu tana kinantuwa (Ba jinin wanda ya fi na wani), dan karaminsu yana tafiya da alkawarinsu kuma hannunsu daya ne a kan wanda ba su ba.
Da fadinsa cewa “mutune kamar bakin talge ce (kurya) – Ma’ana mutane iri daya ne.
- Mawakiyar Yabon Fiyayyen Halitta Annabi (SAW), Rukayat Gawat Ta Rasu
- Fasaha Da Balagar Harshen Manzon Allah (SAW)
Da fadinsa cewa “Almar’u ma’a man a habba – Mutum yana tare da wanda yake so”, “wala kaira fi suhbatin man la ya ra laka, fi ma tara lahu – babu alkairi cikin abota da wanda bai ba da hakkin abota (bai maka zaton abin da kake yi masa zato na alkairi) ba”. Wannan Hadisi ya tattare maganganu da yawa amma ga shi an fade shi cikin Hikima.
Da fadinsa cewa “Wannasu Ma’adinun – Mutane Baramu ne”, Misali ramin zinare, zinare za a yi ta samowa, in karfe ne , karfe kawai za a yi ta samowa, haka Fetur da sauran albarkatun kasa.
Wani mutumin cikinsa kamar zinare ne, alkairai ne kawai a cikinsa, wani kuma azurfa ce acikinsa, itama alkairi ce, wani kuma dalma ce a cikinsa, babu alkairi sai kayan nauyi, wani kuma kwalli ne a cikinsa, ado ne a tare da shi, ko bai amfane ku ba, ado ne. Ma’ana kowa ya zabi Ma’adinin da yake so ya zama, ko ba haka Allah ya halicce ka ba, to yi ta yin kokari ka zama hakan, Duniya ta yi ma shaida cewa ka yi kokarin canzawa. Wannan Hadisi ya isa Hikima.
Da fadinsa cewa “Ma halaka Imru’un Arafa Kadruhu – Mutum Bai halaka ba wanda yasan iyakansa” Ma’ana wanda ya san inda aka ajiye shi kuma ya girmama hakan, ba zai halaka ba.
Da fadinsa cewa “Wal mustasharu, Mu’utamanun – Wanda aka nemi shawararsa, lallai amintacce ne” Ma’ana duk wanda ya zo wajenka ya ce wane ina neman shawara, ma’ana ya amince da kai, to ka ba shi shawara don Zatin Allah, sannan kuma duk wanda aka nemi shawararsa to kamar an bashi zabi ne, in ya so ya ba da shawara in ya so kuma ya ce wane je ka nemi wanda ya fini sanin lamarin matukar ba ka fara cewa komai ba amma in ka fara yin magana sannan ka kafa uzuri cewa ai kaza-da-kaza ko kuma ai ku ba ku karbar shawara to Shari’a ta daura maka wajibi sai ka ba da shawara kuma don Zatin Allah.
Da fadinsa (SAW) cewa “Wa Rahimallahu abdan kala kairan faganima au sakata fasalima – Allah ya jikan bawa, wanda ya fadi alkairi sai ya samu riba Duniya da Lahira ko kuma ya yi shiru sai ya kubuta” Ma’ana Allah ya jikan mutumin da ya yi magana amma ta alkairi, zai samu ribar duniya da ta lahira in kuma ya san maganarsa ba alkairi ba ce sai ya yi shiru, ya kubuta babu mai tuhumarsa da cewa ya ce.
Da fadinsa cewa “Aslim, Taslim, yu’utikallahu ajraka marrataini– Ka Musulunta, ka kubuta sai Allah ya ba ka ladanka sau biyu (ladan ka bi wani Annabin yanzu kuma na zo na yi kira ka bi.”
Da fadinsa “Wa inna ahabbakum ilaiya wa akrabakum minni majalisan yaumal kiyamati, Ahasinukum Akhlakan, Almuwaddi’una aknafan, Allazina ya’alafuna wa Yu’ulafuna – mafi soyuwanku a gare ni kuma mafi kusancinku a gare ni a wajen zama ranar alkiyama shi ne wanda ya fi kyawun dabi’u kuma mai kankan da kai, wanda ya saba da mutane su ma mutane sun saba da shi.”
Haka nan da fadinsa cikin wani zance “… La’allahu kana yatakallamu mimma la ya’anihi, wa yabkalu bi ma la yugnihi– wata kila yana shiga maganar da ba ta dame shi ba kuma yana rowa da abin da ba zai wadace shi ba (kila mutum mai rowa ne kuma yana magana a kan abin da bai dame shi ba).
Da fadinsa cewa “zul wajhaini, la yakunu indallahi wajihan – Mai fuska biyu (Muna fiki) mai hada mutane fada, ya ce kaza a can anjima ya ce kaza a can, ba shi da wata daraja a wurin Allah.”
Yana daga cikin irin wadannan Hadisan Masu Fasaha, Haninsa ga ka ce-na ce, da yawan tambaya, da hana kyauta kai kuma ka ce a miko maka, da saba wa iyaye mata, da bizne ‘ya’ya mata, da tozarta dukiya ba cikin Allah ba. An tambayi Shehu Ibrahim Kaulaha game da almubazzaranci, sai ya ce almubazzaranci, shi ne ka kashe Kobo daya ba cikin Allah ba, in ka ba da Kobo daya cikin barna ka yi almubazzaranci, amma in ka kashe dukiyarka gaba daya cikin Addini ba ka yi almubazzaranci ba, dalilina na fadan haka, shi ne Sayyidina Abubakar ya dauko dukiyarsa gabadaya ya kawo wa Sayyidina Rasulullahi (SAW), Annabi ya ce masa me ka bari a gida ya ce Allah da Annabinsa, Sai Annabi ya ce masa Allah ya yi Albarka. Ka san kuma ba za a yi almubazzaranci a gaban Annabi ya kyale ba.
Yana daga ciki, fadarsa “Ittakillaha haisu ma kunta, wa atbi’issayyi’atil hasanati tamhuha, wa khalikin nasi bi khulukin Hasanin, wa khairil Umuri Ausaduha – Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, sannan ka biyar wa mummuna da aiki kyakkyawa, sai ta shafe mummuna, ka yi mu’amala da mutane da kyakkyawar dabi’a, fiyayyen lamura, tsaka-tsaki”. Malaman Zahiri suka ce “in ka yi sabo a waje, to ka gudu wani wuri ka nemi gafara, don akwai shaidaninka a nan wajen.”
Sufaye suka ce “in ka yi sabo a waje, to da sauri ka yi alwala ka yi alkairi a wajen, in wurin ya kai kara ranar alkiyama ka yi sabo a wajen take a wurin kuma zai fada cewa ka yi alkairi a wajen”.
In ka yi sabo a sarari, to ka fito a sarari ka nemi tuba, haka kuma in ka yi sabo a boye kar ka fito sarari ka tuba, ka tuba a boye da wannan ne ake cewa “in ka bata a sarari, ka gyara a sarari, in ka bata a boye ka gyra a boye.”
Da fadarsa cewa “Ahbib Habibaka haunan ma, Asa an yakuna bagidaka yauman ma, Abgi bagidaka haunan ma, Asa an yakuna habibaka yauman ma – Ka so Masoyinka cikin sauki-sauki, wata rana yakan iya zama makiyinka, kuma ka ki makiyinka kadan-kadan, wata rana yakan iya zama masoyinka.” Wannan ba soyayya da aka hadu cikin Allah ba, ana nufin abokinka da kuka hadu cikin wata harka, kar ka dauki asararanka ka mika masa, kuma kar ka ki shi sosai, ka yi ta masa jafa’i don wata rana Allah mai iko ne ya mai da shi cikakkken masoyinka.
Da fadarsa cewa “Azzulmu zulmatun – Zalumci Duhu ne” duk mai son duhun ranar alkiyama da duhun kabari to ya dinga zalumci, wanda yake so ya tashi cikin Haske ranar alkiyama to kar ya yi zalunci, zai hadu da Allah lami-lafiya.
Da fadinsa a cikin wani yanki na Addu’arsa “Allahumma inni as’aluka rahmatan min indika tahdi biha kalbi, wa tajma’u biha umuri, watalumma biha sha’asi, watuslihu biha ga’ibi, watarfa’u biha shahidi, watuzakki biha Amali, watulhimuni biha rushdi, waturuddu biha ulkati, wata’asimuni biha min kulli su’in, Allahumma inni as’alukal fauza indal kada’i wa nuzulash shuhada’i – Allah ina rokon ka rahamarka da za ta shiryar min da zuciyata, kuma ta tattaro min lamurana, kuma ta tattaro min rarrabewa ta, kuma ta gyara min duk wanda ya faku gare ni na daga ‘ya’ya da duk abin da baya tare da ni, kuma ta daga darajar duk wanda yake tare da ni, kuma ta tsarkake min ayyukana, kuma Allah ka kintsa min shiriyata da ita sannan Allah ka mayar min da sabona, ka tsare ni daga dukkan mummuna, Ya Ubangiji ina rokonka samun babban rabo yayin hukuncinka da mutuwar Shahidai.”
Mutuwar Shahada ba dole sai a wurin yaki ba, mutuwar mutum da Kalmar Shahada, shahada ce, mutuwa da Ma’arifa, mutuwar Ciwon ciki, mutuwar konewar wuta, mutuwar rushewar gini da duk wata mutuwar da ta fi karfinka ba kai ka janyo ta ba, Shahada ce.