An rufe taron mutum-mutumin inji na duniya na 2025 yau 12 ga watan Agusta a birnin Beijing na Sin. Mahalarta daga ciki da wajen kasar Sin, ciki har da ‘yan Afirka, sun ga saurin ci gaban masana’antar fasahohin AI ta Sin da kuma sabbin abubuwan kirkire-kirkire.
A halin yanzu, bukatar bunkasa fasahohin AI a kasashen Afirka na karuwa cikin sauri, yayin da karfin fasahar AI na Sin ke kara ingantuwa, wanda ke baiwa sauran kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka damar samun bunkasuwa bisa karfin AI. Alkaluman da aka bayar na nuna cewa, Afirka ta zama yanki na biyu mafi saurin karuwar amfani da AI a duniya. Dandalin kididdiga na Afirka ya nuna cewa a shekarar 2023, manhajoji 141 na wayar hannu masu alaka da fasahar AI sun bullo a kasuwar Afirka, wanda ya karu da kashi 24 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Kana matsakaicin adadin masu amfani da manhajojin AI a kowane wata ya zarce miliyan 40. Manufar tattalin arzikin dijital ta Najeriya daga shekarar 2020 zuwa 2030 ta nuna cewa za a kafa cibiyar AI da mutum-mutumin inji ta kasa a nan gaba.
A cikin ‘yan shekarun nan, Sin da Afirka sun samar da ingantacciyar hadin gwiwa a fannin AI ta hanyar wasu tsare-tsare na kasashe biyu da na kasashe da dama, wanda ya zama muhimmin abu mafi jawo hankulan mutane a cikin hadin gwiwar Sin da Afirka. Wasu kamfanoni na Sin sun taka rawar gani wajen bunkasa kayayyakin more rayuwa na dijital a kasashen Afirka, suna ba da damar daidaita ayyuka, da hidimomi na zuba jari a fannin AI, abin da ya sa dimbin ‘yan Afirka cin gajiyarsu. A yanzu, Sin ba kawai ta zama daya daga cikin manyan kasashen da ke fitar da fasahar AI da kayayyaki zuwa Afirka ba, har ma ta hanyar kafa cibiyoyi, tana horar da matasan Afirka ilimin AI iri-iri.
Lokacin da bukatun Afirka suka hadu da karfin Sin, muna da dalilin yin imani cewa, tare da tallafin dandalolin kamar su “dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC)” da shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin gwiwar AI tsakanin Sin da Afirka tabbas za ta samar da samako mai armashi nan gaba. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp