Sojojin Nijeriya biyar ne suka mutu bayan da motarsu ta taka wata nakiya da ake zargin mayakan jihadi ne suka birne a kusa da kan iyakar Nijar, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana.
Rundunar ta kasance cikin sintiri na yau da kullun a kauyen Laayi da ke kusa da garin Damasak a ranar Litinin din da ta gabata lokacin da suka taka wata nakiya, kamar yadda wasu shugabannin mayakan biyu suka shaida wa AFP.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Dirar Mikiya Wurin Taro, Sun Kashe Shugaban Al’umma A ImoÂ
- Kotun Sauraron Kararrakin Zabe Ta Fara Zama A Kebbi
Sojojin sun tayar da wasu bama-bamai da ake zargin kungiyar IS da ta kafa daular Islama ta yammacin Afirka (ISWAP) ce ta saka, in ji shugaban mayakan Babakura Kolo.
Fashewar “Ta kashe duka sojojin biyar da ke cikin motar”, in ji shi.
Kolo ya ce mayakan jihadin sun kai hari kauyen ne a daren jiya, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna kauyen hudu da suka hada da shugaban karamar hukumar tare da dasa bama-baman yayin da suke barin kauyen.
Mai magana da yawun sojojin bai amsa kiran da AFP ta yi ba don jin ta bakinsa game da lamarin.
Shugaban ‘yan ta’adda na biyu, Ibrahim Liman, ya bayar da kididdigar adadin wadanda suka mutu.
ISWAP da ta balle daga kungiyar Boko Haram mai da’awar jihadi a shekarar 2016 ta zama babbar barazana a Nijeriya, inda ta kai hari kan sojoji da ke sintiri yayin da suke kashewa tare da yin garkuwa da fasinjoji a shingayen bincike.
Bangarorin biyu masu gaba da juna na masu jihadi sun gwabza fada a cikin ‘yan watannin da suka gabata yayin da sojoji suka zafafa kai hare-hare kan kungiyoyin.
An kafa sojojin ne a manyan sansanoni da aka fi sani a fadin yankin, lamarin da ya bar wasu kauyuka da yankunan karkara ba su da kariya da kuma fuskantar hare-hare.
A watan da ya gabata sojoji uku ne suka mutu sannan wasu hudu suka jikkata tare da wasu fararen hula bakwai a wani fashewar nakiya da ta tashi a kan wata motar soji a wajen garin Banki da ke kusa da kan iyaka da Kamaru.
Rikicin da aka kwashe shekaru 14 ana yi ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 40,000 tare da raba sama da miliyan biyu da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Rikicin dai ya bazu zuwa wasu sassan kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da ke makwabtaka da Nijeriya, lamarin da ya sa rundunar hadin gwiwar sojojin yankin ke yaki da mayakan.