Kungiyar ‘yan ta’adda ta ‘Islamic State of the West African Province’ (ISWAP) ta yi garkuwa da ma’aikata masu taimakon jin kai da suke aiki da wata kungiyar taimakon kiwon lafiya ya kasa da kasa wato ‘Family Health International’ (FHI 360) su uku tare da jami’an tsaron su biyu a Arewa Maso Gabas na Ngala da ke jihar Borno.
Kungiyar FHI 360 wata kungiyar taimakon al’umma ta bangaren cigabansu ce da ta maida hankali wajen bunkasa kiwon lafiyan jama’a musamman a Arewa Maso Gabas.
An nakalto cewa adadin ‘yan ta’addan da ba a tantance ko su nawa ba ne, sun kutsa kai zuwa gidan kungiyar a wani harin boye da suka yi a ranar Laraba da karfe 4 na safiya tare da yin awun gaba da ma’aikatan zuwa wani wajen da ba a sani ba.
Zagazola Makama, wani kwararren mai nazarin lamuran tsaro a yankin Lake Chad, shi ne ya tsogunta batun garkuwa da ma’aikatan tare da masu musu hidimar tsaro.
Har zuwa yanzu dai kungiyar ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.